‘Zan iya sayar da gidana don biyan ƴan fashi su sako min ƴata’
Iyayen ɗaliban Kwalejin Yawuri a Najeriya waɗanda har yanzu ƴaƴansu ke tsare a hannun ƴan fashin sun ce sun shiga ƙarin firgici saboda sun daina yin da ƴaƴan nasu.
Tsawon shekara ɗaya da wata takwas ke nan ƴan matan su 11 na a hannun ƴan bindiga tun bayan da aka yi garkuwa da su daga kwalejin gwamnatin tarayya ta Yauri.
Iyayen sun ce matakin ya zo ne bayan riƙaƙƙen ɗan fashin da ke garkuwa da ɗaliban, ya nemi su biya wasu maƙudan miliyoyin naira, kafin ya sake su.
Sun bayyana takaicin cewa hukumomin jihar Kebbi sun yi watsi da lamarinsu, don haka suka buƙaci ɗauki daga sauran al’ummar gari, don ganin an kuɓutar da ƴaƴan nasu.
Ɗaya daga cikin iyayen ɗaliban ta faɗa wa BBC cewa a yanzu ƴan fashin dajin sun katse duk wata hanyar sadarwa tsakaninsu da ƴaƴansu, saɓanin yadda a baya kusan kullum suke magana su.
Ta ce ƴan fashin sun sanar da su cewa sun daƙile duk wata dama ta ji daga ɗaliban har sai sun biya su kuɗaɗen da suka nema.
Salim Ka’oje, shugaban iyayen ragowar ɗaliban kwalejin Yauri, ya bayyana cewa a baya, sun ɗan samu ci gaba “can dama bai yadda mu shigo a matsayinmu na iyaye a daidaita da mu ba,”
“Yanzu ya yadda mu shigo kuma har ya kai ga matsayar abin da yake buƙata a yi masa, kuma ina kyautata zaton waɗanda ke mana ƙoƙari zuwa ga gwamnati, sun je sun kai wannan kuka namu amma shiru.”
Sai dai ya ce riƙaƙƙen ɗan fashin dajin ya tuntuɓe shi a waya, inda ya bayyana masa cewa matuƙar suka gaza ba shi abin da ya nema a wajensu, toh “mu tabbatar mu da yaranmu sai lahira.”
Mahaifan ɗaliban 11 dai sun ce sun yanke ƙauna kan hukumomi saboda biris ɗin da aka yi da su.
Niyanthara Daniel, ɗaya daga cikin iyayen ƴan matan, ta ce tana iya sayar da gidansu na kwana domin ganin ta kuɓutar da ƴarta.
Ta ce “Ni dai gaskiya ba ni da wani abu, sai ɗan gidan da muke ciki, in ya kama ma mu sayar da muhallinmu ne, sai mu sayar.”
Ta ƙara da cewa za su nemi taimakon ƴan uwa da al’ummar gari , “ko bara za mu yi, mu haɗa da abin da Ubangiji ya hore mana mu bayar, tun da gwamnati dai, mun yi jira, mun yi jira har yanzu ba magana.”
A cewarta, gwamnati ba ta kira su ko ta yi masu wani bayani ba game da irin ƙoƙarin da suke yi na ganin an kuɓutar masu da ƴaƴansu.
“Gwamnan Kebbi a jiharsa ce aka kwashe yaranmu, har yau bai taɓa kiranmu ya ba mu magana, mu ji ɗan dama-dama ga zuciyarmu ba.” kamar yadda mahaifiyar ta faɗa.
Ƴan fashin daji a Najeriya sun sha sace ɗaruruwan ɗalibai amma ana kuɓutar da su, sai dai baya ga ƴan matan Chibok, babu ɗaliban da suka fi ƴan matan Yauri daɗewa a hannun ƴan bindiga.
Zai yi wuya a iya hasashen dalilin da ya sa hukumomi suka yi biris da wadannan ƙananan yara ƴan makaranta, kamar yadda iyayensu ke iƙirari.