Zan ƙirƙiri ‘yan sandan jihohi idan na zama shugban ƙasa – Aminu Tambuwal.
Gwamnan Jihar Sokoto a arewacin Najeriya Aminu Waziri Tambuwal ya ce aikin ɗan sanda yana da muhimmanci sosai ga tsaron Najeriya, abin da ya sa zai ƙirƙirii ‘yan sandan jihohi idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2023.
Da yake magana ta cikin shirin Politics Today na Channels TV ranar Talata, Tambuwal ya ce “wajibi ne a yi maganin matsalar tsaro tun daga tushe”.
A cewarsa: “Ina da tsarin yadda za a yi. Dole ne mu mayar da abin [tsaro] ga matakin al’umma. Dole mu tattauna kan ‘yan sandan jihohi, mu matso da tsaro ksua da al’umma.”
Da aka tambaye shi ko zai gabatar da ƙudirin neman kafa dokar ‘yan sandan jihohi ga majalisa, ya tabbatar da cewa zai yi hakan.
“Idan ta kama ni a matsayina na shugaban ƙasa zan iya ɗaukar ƙudirin da kaina na kai wa shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisa. Saboda na yi imanin yana ɗaya daga cikin abubuwan da muke buƙata da gaggawa don kawo ƙarshen matsalar tsaro.”
READ MORE : Rahotannin game da yaƙi a Ukraine zuwa yanzu…
Gwamna Aminu Tambuwal na neman samun tikitin takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar adawa ta PDP, inda zai fafata da irinsu Atiku Abubakar da Bukola Saraki da Gwamna Bala Muhammed na Bauchi.
An daɗe ana muwahara game da dacewa ko akasin haka ta kafa ‘yan sandan jihohi a Najeriya, abin da a yanzu haka kundin tsarin mulkin ƙasar bai ba da dama ba, inda gwamnatin tarayya ce kaɗai ke iko da ‘yan sandan.