Wasu ‘yan bindiga a ranar Asabar sun kashe akalla mutane 25 a wani hari da suka kai wasu kauyuka biyu a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.
Hare-haren sun zo ne mako guda bayan da ‘yan bindigar suka kashe fiye da mutane 25 da suka hada da ‘yan banga 16 a gundumar Kanoma da ke karamar hukumar Maru.
Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, wasu ‘yan bindiga sun mamaye kauyen Janbako kuma sun harbe sama da mutum 20.
“Sun isa kauyen ne a kan babura da misalin karfe 2 na rana, suka bude wa mazauna kauyen wuta.
“Bayan haka, ‘yan ta’addan dauke da makamai sun koma yankin Sakkida suka harbe mutum biyar a can,” inji Buhari Saminu mazaunin garin.
ake ciki, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana harin a matsayin dabbanci karara.
Ya ce, gwamnatinsa ba za ta nade hannunta ba, ta bar ‘yan ta’adda suna kashe al’umma ba gaira ba dalili ba.
A wani labari na daban sama da mutum hamsin ne aka bada labarin cewa ‘yan bindiga dadi sun kashe a kananan hukumomi biyu da suke jihar Sokoto a daren ranar Asabar.
Kananan hukumomin da lamarin ya faru a cikinsu su ne Gwadabawa da Tangaza dukka da suke jihar.
Kakakin hukumar ‘yansandan jihar Sokoto, ASP Ahmad Rufa’i, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, ya bada tabbacin hukumar na kan binciken lamarin, kuma sun sha alwashin cewa za su sanar da ‘yan jarida karin bayanin da bincikensu ya nuna musu.
da harin a yankuna uku da suke karamar hukumar Tangaza, gawarwaki 37 har yanzu ba a musu biso ba.
Yankunan da aka kai wa harin a daren ranar Asabar sun hada da Raka, Raka Dutse, da Filin Gawa da suke karamar hukumar Tangaza.
Tsohon shugaban karamar hukumar Tangaza, Bshar Kalenjeni ya tabbatar da cewa harin ya kashe18 a kauyen Raka, 17 kuma a Filin Gawa sai mutum biyu a Raka Dutse.
Wata majiya a Gwadabawa ta shaida ma wakilinmu cewa ‘yan bindigan sun kasance a yankin inda suka yi nazarin yadda za su kaddamar da harinsu ba tare da al’ummar garin sun sani ba.
“Sun hara kai harin ne bayan kammala sallar Isha’i inda suka kai wa shahararrun kauyuka biyu hari da Sakamaru da kauyen Bilingawa.
“A Bilingawa, sun kashe a kalla mutum 18, a Sakamaru Kuma abun ya kasanta domin yankan rago suka yi tabui wa mutane wasu kuma suka bindigesu. Sun yanka mutane kamar dabbobi suka Kuma konasu ta yadda ba ma a iya Gane waye wannan waye wancan,” ya shaida.