Yan bindiga sun kai mummunan hari kan kauyen Mutunji da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
Mahara sun kai harin kautan bauna a ranar Lahadi inda suka kashe sojoji 10 da fararen hula 68.
A halin da ake ciki babu wani cikakken bayani daga hukumomin sojoji da yan sanda kan al’amarin.
Nigerian Tribune ta rahoto cewa akalla sojoji 10 da mazauna 68 ne suka mutu a ranar Lahadi, 18 ga watan Disamba, sakamakon wani hari da yan bindiga suka kai kauyen Mutunji na masarautar da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
An rahoto cewa an kwashi gawarwakin sojojin da aka kashe zuwa asibitin kwararru na Yariman Bakura da ke Gusau, babban birnin jihar ta Zamfara.
Maharan sun kaiwa sojojin da ke tabbatar da zaman lafiya a yankin kautan bauna a hanyarsu ta zuwa dakile wani hari a kan kauyen Mutunji.
TVC News ta rahoto cewa fiye da mutane 40 ne suka ji munanan rauni inda a yanzu suke samun kulawar likitoci a babban asibitin Dansadau da asibitin kwararru na Yariman Bakura.
Garin Dansadau na kilomita 104 daga Gusau, babban birnin jihar Zamfara kuma yana daya daga cikin manyan wuraren da ke fama da ta’addanci da sace-sacen mutane a yankin arewa maso yamma.
Dajin Dansadau na da girma kuma yana da iyaka da jihohin Kaduna, Sokoto Kebbi da Neja.
An sha yin awon gaba da mutane a lokuta mabanbata yayin da jami’an tsaro ke ceto su wasu kuma wadanda suka yi garkuwa da su ke sako su don ra’ayin kansu.
Martanin rundunar soji da na yan sanda Duk wani kokari da aka yi don jin ta bakin hukumomin sojoji da na yan sanda a jihar Zamfara ya ci tura domin kakakin hukumomin tsaron biyu basu amsa kiran waya ba.
A wani labari na daban, dakarun rundunar sojojin Najeriya sun yi nasarar halaka mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram da yawa a jihar Borno.
Dakarun Operation Hadin Kai sun farmakin mayakan a kauyen Ngowom da ke karamar hukumar Mafa a hanyarsu ta zuwa dajin Sambisa.
Source:LegitHausa