Miyagun ‘yan bindiga sun kai sabon mummunan hari kan bayin Allah a garin Tauji dake karamar hukumar Maru a Zamfara.
Bayanai sun yi nuni cewa mutum uku sun rasa rayuwarsu yayin da maharan suka sace mata masu shayarwa guda Takwas.
Wannan na zuwa ne a lokacin da Sojoji ke ci gaba da kai samame maɓoyar ‘yan ta’adda a sassan jihar.
Aƙalla mutum uku suka rasa rayukansu kuma aka sace mata masu shayarwa Takwas yayin da wasu yan bindiga suka kai hari yankin Tauji, Kanoma ta arewa, ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.
Wani ɗan asalin yankin, Muhammad Maisa, wanda ya zanta da jaridar Punch, yace lamarin ya faru da misalin ƙarfe 1:40 na dare lokacin da wasu sanannun ‘yan bindiga suka shigo yankin.
Maisa ya bayyana cewa da zuwan ‘yan bindigan a kan Babura ba wata-wata suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi domin su tsoratar da mutane.
Mutumin yace: “Daga nan sai suka riƙa kutsawa gida-gida suna neman mutanen da zasu yi garkuwa da su.
Sun yi nasarar tafiya da matan aure Takwas, ma fi yawansu suna shayarwa, sannan kuma suka kashe mutum uku da suka yi yunkurin tsere wa.”
Basaraken garin, Alhaji Ibrahim Nabature (Sarkin Sudan) ya tabbatar da kai sabon harin.
Ya yi kira ga gwamnatin Zamfara ta ƙara girke jami’an tsaro a yankin don kare hare-haren yan ta’adda.
Duk wani yunkuri domin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda reshen Zamfara, Muhammad Shehu, bai kai ga nasara ba domin lambarsa ba ta shiga sam.
Zamfara na ɗaya daga cikin johohin da ke fama da ayyukan ta’addancin ‘yan bindiga a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
A wani labarin kuma Kasurgumin Dan Bindiga, Bello Turji, Ya Maida Martani Kan Harin da Jirgin Sojin Najeriya Ya Kai Gidansa a Zamfara Sanannen ɗan bindigan nan, Bello Turji, ya nuna damuwarsa bisa harin da jirgin sojoji ya kai gidansa a Zamfara.
Turji yace harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutanensa da dama duk da ya tuba ya rungumi zaman lafiya tsawon watanni.
Source: LEGITHAUSA