Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce ya jajanta wa Bola Tinubu game da zamewar da ya yi lokacin hawa mota har ya fadi.
“Ina matukar jajanta wa shugaba Bola Tinubu dangane da dan hatsarin da ya samu a lokaci da yake kokarin zagaya masu fareti a ranar dimokaradiyya. Ina fatan lafiyarsa kalau yanzu.”
A ‘yan kwanakin nan Atiku na ci gaba da sukar shugaba Tinubu kan wasu ayyukansa da jam’iyyar ta APC.
Ko a jiya Talata sai da jami’yyar PDP ta soki Tinubu, inda ta ce ‘yan Nijeriya a fusace suke kan irin manufofin da gwamnatinsa ke kaddamarwa.
A gefe guda kuma har yanzu babu wani martani daga gwamnati mai ci kan jajen zamewar da Atiku yayi Tinubu.
A wani labarin na daban shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, na shirin yin garambawul a majalisar ministocinsa, inda ake sa ran zai nada sabbin ministoci, da kuma samar da sababbin ma’aikatu da kuma yunkurin samar da ma’aikatar da za ta kula da kebe da kuma bunƙasa harkar kiwon dabbobi.
Wannan ma’aikatar dai za ta kasance a karkashin Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara.
Baya ga samar da wannan sabuwar ma’aikata, Tinubu na shirin nada kananun ministocin a ma’aikatu da ba su da ƙananan minista.
Ministocin da za a samar musu da ƙananan ministocin sun haɗa da na Ayyuka da Kwadago da Ma’aikatar Jin kai da Rage Talauci.
Sauran sun haɗa da Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama da Ma’aikatar Makamashi da Ma’aikatar Kula da Al’adu da Ɓunkasa Tarihi.
DUBA NAN: Kotu Ta Yankewa Matar Alkali Hukuncin Kisa Bisa Laifin Kashe Shi
Sauye-sauyen ya biyo bayan tantance ayyukan ministoci da shugaba Tinubu ya yi.