Shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da Zamantakewa ta rayuwar yau da kullum, zaman Aure, Rayuwar Matasa, Soyayya da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yadda wasu mutanen ke baje kolin hajar bayyana sirrikansu da zarar sun hau abun hawa, musamman mata.
Sau tari a kan samu hakan daga wajen wasu matan yayin da suka shiga abun hawa sai su maida shi tamkar a tsakiyar falon gidajensu, wanda ya ke tafe a kasa ma yana jin hirar da suke yi, haka wanda ke cikin wata motar ma duk yana jinsu, ba sa tuna komai yayin da suke baje hajar ta su.
Dalilin hakan ya sa shafin Taskira jin ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu; Ko mene ne amfani ko rashin amfanin hakan?, wadanne irin matsaloli hakan ka iya haifarwa?, ta wacce hanya za a iya magance afkuwar hakan?. Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sunana Hadiza Ibrahim D. Auta. Kaura-Namoda Jihar Zamfara:
Mata
Tabbas mu mata muna da wannan halin, wanda akasarinmu hira ba ta dadi har sai an shiga Napep.
Wanda kafin a kai inda ake son zuwa an baje kolin sirrukan da bai dace a watsar da su duka a cikin wannan dan tsukakken lokaci ba. Saboda ko daga masu hirar sai mai Napep suka yi aringizon fesar da abin da ke cikin bakunansu; to abin zai yi musu babbar illa, irin wacce ba za su taba zaton za su girbe abin da suka shuka a cikin wasu takaitattun dakikun da ba su wuce a kirga da yatsun hannu lba. Saboda ba kowace magana ce za ta yi wa mutum amfani a irin wannan lokacin ba. Amma wata idan an yi za iya ta ceto mutum daga halaka, yayin da wata idan an fasa rubabben ƙwai take zame wa mutum musiba da tonon asiri. Misali; akwai wata da ta dauko maita, suna tafe cikin Napep ita da kawarta.
Suka fara tambayar juna kurwa nawa suka samo, daya ta ce ba su da yawa, daya ta ce ita kam ta samo da yawa. Don a cikin jakarta har da kurwar mahaifinta akwai. Har mai Napep ya ajiye su gidajensu, amma ya kasa natsuwa saboda tashin hankalin hirarsu da kunnensa ya debo masa.
Jikinsa yana rawa ya koma gidansu wacce ta samo da yawa, ya yi sallama ya ce mai gidan yake nema. Aka ce da shi mai gidan bai da lafiya tsawon kwanaki ba zai iya fitowa ba.
A take ya nemi ganin matar gidan, bai boye komai ba ya yi bayanin abin da kunnensa ya ji. Aka saka yarinya gaba ta bude jakar da ta saka kurwowin, sai ga fari suna ta fita a ciki suna tashi. Mintuna a tsakani mahaifinta ya mike daga zazzafan ciwon da ya kama shi.
‘Yan gidan da mutanen unguwa suka dinga jibgar yarinyar. Kafin dan lokaci unguwa ta karade da labari. Abun duba a nan, hira a Napep ta yi wa mahaifinta rana, kuma ita ta janyo mata falluwar sirri da jin kunya bayan kalolin tozarcin da za ta fuskanta a sanadin hakan.
Babban hanyar magance wannan matsalar kame kai a ko’ina da kame baki muddin ba muhallin da ya dace ba. Shawara ga masu irin wannan halin; su daina, duk yadda zance ya matsi bakinsu su yi kokarin rufe abin su har sai sun fita Napep su furzar.
Saboda wani daga lokacin da ya ji wani abu daga bakinka; to a duk lokacin da ya sake ganin ka ko ya ji labarin ka sai ya ce ai da bakinta ma na ji ta ce kaza.
Allah ya ba mu ikon killace abin da ke zuciyarmu da bakinmu a wurin wadanda suka dace da inda ya dace mu fada.
Source LEADERSHIPHAUSA