‘Yan uwa musulmi almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky wadanda aka fi sani da ‘yan shi’a sun gudanar Muzahara domin kira ga hukumomin da abin ya shafa su saki takardun tafiyar malamin su domin fita kasashen ketare neman lafiya.
Wannan na kunshe ne a cikin wani bidiyo da kafar sadarwa ta ABS CHANNEL ta saki wanda ya bayyana mambobin harkar musulunci a Najeriya din suna gudanar da zanga zangar lumanar tattare da rera wakokin kira da a saki takardun tafiyar malamin nasu.
Muzaharar wacce aka bayyana an gudanar da ita a babban birnin tarayyar Abuja kuma an isar da ita har cibiyar kare hakkin dan adam (Human rights commision Abuja) babban hadafin ta shine ankarar wadanda abin ya shafa su gaggauta sakin fasfon malamin kamar yadda hakan ‘yancin sa ne.
‘Yan uwa almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky dai na zargin wasu hukumomi da rike takardun tafiyar shehin malamin wanda aka bayyana yana fama da rashin lafiya kuma yana bukatar fita kasashen ketare domin a duba lafiyar sa.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa kwamitin lauyoyin harkar ta musulunci a Najeriya sun shigar da kara a wata babbar kotu Abuja amma sai dai kotun ta sallami karar bisa wasu dalilai data bayyana.
Sai dai a nasa bangaren daya daga cikin lauyoyin harkar ta musulunci a wata fira da manema labarai ya bayyana wannan hukiunci da kotu tayi matsayin rashin fahimtar su inda ya bayyana dalilin da alkali ya bayar na sallamar wannan kara ba karbabbe bane.
Da aka tambaye shi game da shigar da wata karar ya bayyana cewa farko lauyoyi zasu nazarci wannan hukunci kafin daga bisani Sheikh Zakzaky a matsayin sa na wanda yake kara zai duba yiwuwar shigar da wata karar.
Zuwa yanzu an gudanar da ire iren wadannan zanga zangar ta lumana a garuruwa mabambanta duk domin tabbatar da gwamnati ta saki fasfon malamin domin tafiya neman lafiya.