A rahoton da kafar sadarwa ta ABS CHANNEL ta rawaito na jawabin kai tsaye da jagoran harkar musulunci a Najeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky ya gabatar a wajen mu’utamar na kasa wanda aka gabatar a garin katsina ranar 27 zuwa 29 ga watan janairu shekarar 2023.
Jagoran a farkon jawabin sa ya bayyana muhimmancin tunani a rayuwar mutum inda yace “Duk Ayyukan Mutum Yakan Faru Sakamakon Yadda Yake Tunanin Sa”.
Shehin malamin ya bayyana yadda addinin Musulunci yayi horo da tunani domin tunani na dan gajeren lokaci ya kan iya canja rayuwar mutum ta fuska mai kyau ko akasin hakan, hakan ne ma ya sa aka samu hadisi da yake bayanin cewa “Tunanin sa’a daya yafi ibadar shekara”.
Malam Zakzaky ya bayyana wannan taro na mu’utamar a matsayin wata hanya ta kwakwkwafe tunani wanda yace hakan yana da matukar muhimmanci, ya kuma cigaba da cewa mutum yana da bukatar lokaci bayan lokaci ya rika samun kwakwkwfewar tunani.
Da ya juya banagren tarihin nahiyar mu Sheikh Zakzaky ya bayyana cewa, mu a nan muna da kabilu wadanda suke da yanayin su na ‘ya’yan wane da ‘ya’yan wane, a kwai kuma wadanda sakaamkon zama suka dade har ko dai sun mance asalin su ko kuma suna ganin kansu a matsayin guda ne.
Shehin ya bayyan cewa, suma wadannan suna da harshe iri guda da kuma al’adu iri guda suma muna kiran su kabila, amma da bature yazo sai ya zo da irin tunanin sa na kabilancin sa’annan ya dube mu ya kuma bamu sunan da shi baya kiran kansa da hakan.
A karshen jawabin sa shehin malamin yayi kira ga dakewa bisa tafarkin Allah da kuma kira zuwa komawa tafarkin Allah har zuwa karshen rayuwa.
Ya kuma bayyana yaduwar fahimtar tafarkin Ahlulbayty (S.a) a matsayin wata alama da take bayyana kusantowar bayyanar Imam Mahdi (A.j.t.f.s) wanda da bayyanar sa ne komai zai zama dai dai.