Kamar yadda jaridar Punch ta rawaito zuwa yanzu ana iya cewa an samu nasarar soma shirye shirye domin sabunta fafunan tafiya na babban shehin malamin nan kuma shugaban mabiya darikar shi’a na afirka watau Malam Ibrahim Yaqoob Zakzaky.
Shehin malamain wanda shine jagoran ‘yan uwa na harka isalamkiyya a najeriya ya samu kubuta daga hannun hukuma ne bayan da kotu ta wanke shi daga laifukan da ake zargin sa dashi.
Malam zakzaky da mai dakin sa malama zinatuddin sun shafe sama da shekara biyar a tsare kuma ana karanta musu tuhumomi amma a ‘yan watannin da suka gabata ne babbar kotun gwamnatin tarayya a jihar kaduna ta tabbatar cewa malamin da mai dakin sa basu aikata laifin komi ba kuma ta sake shi, wanda wannan sakin ne ya kawo karshen zaman gidan yari da suka shafe shekaru sunayi amma sai dai koda malam zakzaky ya fito daga gidan yarin ya bukaci fasfo din sa domin tafiya kasashen ketare neman magani sai abin yaci tura.
Rahotanni danagane da batan dabon fasfo din malam zakzaky da mai dakin sa sun tabbatar da cewa tun wancan lokaci da malamin ya fita zuwa kasar indiya domin duba lafiyar sa fasfon nasa ke hannun hukumomi wanda a yanzu daya bukata ta bayyana fasfo yayi batan dabo.
An shiga halin taraddudi domin gudun kada almajiran malamin su dawo tituna domin cigaba da muzaharorin lumana amma bisa taimakon Allah ta’ala rahotannin da suke zuwa mana suna nuni da cewa a kwai yiwuwar za’a sake ma shehin malamin sabon fasfo shi da mai dakin sa domin su shilla zuwa ketare domin neman lafiya.
”Muna fatan da gaske ne za’a yima malam da malama sabbin fasfuna domin su tafi neman lafiyar su hankalin kowa ya kwanta” kamar yadda daya daga cikin almajiran malamin ya shaida mana a wata fira da mukayi dashi.