Rahotanni daga kasar Saudiyya, sun ce yawan mutanen da suka rasa rayukansu a dalilin tsananin zafi yayin gudanar da aikin Hajjin bana, ya zarce 900.
Tun da farko dai mutane 550 jami’ai suka sanar da mutuwarsu a dalilin zafin da makinsa ya kai digiri 51.8 a kan ma’aunin Celcius.
Matsanancin zafi da aka fuskanta a ayayin gudanar da aikin hajin bana, ya yi sanadiyyar rasa rayuwaka da yawa kamar yadda wasu majiyoyi suka ruwaito.
Majiyarmu ta ruwaito mana cewar, daga cikin mutanen da suka mutu, 323 ‘yan kasar Masar ne, 60 daga Jordan yayinda Iran ke da mutum biyar tare da cututtukan da ke da alaka da zafi.
Alhazan, sun gudanar da aikin hajjin da tallafin hukumomin da ke raba musu kayayakin rage zafi da suka hada da ruwan sanyi lemuka da sauransu.
Hukumomin kasar dai sun bayar da shawara ga alhazai da su dinga amfani da lema, da kuma guje wa shiga rana idan ta take, duk da yawancin ayyukan ibada na buƙatar tsawaitar lokaci.
DUBA NAN: Sojoji Sun Hallaka Kasurgumin Dan Bindiga A Iyakar Kaduna Da Kastina
Ministan lafiya na Saudiyya, Fahad bin Abdul Rahman Al-Jalajel, ya bayar da sanarwar samun nasarar matakan da suka dauka na kiwon lafiya .