Zaben Gambia; Jam’iyyar NPP Ta Samu Kujeru 19 Daga Cikin 53 A Majalisa.
Jam’iyyar Barrow ta National People’s Party ta lashe kujeru 19 daga cikin kujeru 53 na ‘yan majalisar dokokin kasar da aka fafata, lamarin da ya kawar da rinjayen babbar jam’iyyar adawa ta United Democratic Party, a cewar sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta Gambia ta wallafa.
Shugaban kasar na iya nada wasu ‘yan majalisar guda biyar da suka hada da kakakin majalisar, wadanda za a zaba daga jam’iyyarsa nan da kwanaki masu zuwa, amma ya gaza samun cikakken rinjaye a majalisar mai kujeru 58.
Jam’iyyar UDP ta samu kujeru 15 sannan kuma masu zaman kansu sun zo na uku da 11.
Barrow ya lashe zaben shugaban kasa karo na biyu bayan ya doke Ousainou Darboe a zaben shugaban kasar da aka gudanar a bara da kashi 53 cikin 100 na kuri’un da aka kada, a karon farko da kasar ta mika mulki a hukumance kuam a dimukradiyance tun bayan mulkin tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh.
Nasarar da ya yi ba zato ba tsammani a zaben shugaban kasa na 2017 ya kawo karshen mulkin Jammeh na tsawon shekaru 20.
Ba kamar zaben watan Disamba na 2021 ba, inda aka samu karancin fitowar masu kada kuri’a a zaben ‘yan majalisa kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida suka ambata, da kuma kididdigar da hukumar zaben kasar ta bayar.