Gwamnonin Jami’iyyar APC na Arewa sun karyata zargin da ake musu na cewa daukar Kashim Shetiima a matsyin abokin takara a zaben mai zuwa
Tinubu bai musu dadi ba Gwamnonin sun ce suna goyon zabin da aka yi wa Kashim Shettima dari bisa dari saboda shi ma tsohon gwamna ne.
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa, ya ce za su yi aiki tukurun dan ganin jam’iyyar APC ta yi nasara a zaben 2023.
Gwamnoni Jami’iyyar APC na Arewa sun karyata zargin da ake musu na cewa daukar Kashim Shetiima da Tinubu yayi a matsayin abokin takarar sa na zaben 2023 bai musu dadi ba.
Rahoton BBC Gwamnonin sun ce suna goyon zabin da aka yi wa Kashim Shettima dari bisa dari saboda shi ma tsohon gwamna ne.
A hirar da BBC tayi, da gwamnan jihar Gombe Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, ya ce suna goyon bayan zabin Shettima, kuma za su yi aiki tukurun dan ganin jam’iyarsu ta yi nasara a zaben 2023.
“Ai Kashim namu ne, kuma ba za mu ki shi saboda dalilai da dama.
Asiwaju da Shettima sun rike mukamin gwamna, kuma sun yi sanata, don haka sun taba duniyar biyu gabaki daya.
”Babu wanda za ka taba a cikinsu da ba shi da kwarewar da zai taimaka wajen samun nasara da ci gaba a kasar.
“Kuma na tabbatar da dukkanin gwamnonin jam’iyarm APC za su bayar da hadin kan dan ganin anyi nasara.”
Alhaji Inuwa, ya ce daukar Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu ba shi bane damuwarsu. damuwarsu shi ne jam’iyyar APC ta kai ga nasara a zaben 2023 shikenan.
Bayan Ganawa a Landan, Gwamnonin PDP Hudu Sun Amince Su cigaba da zama.
A wani labari kuma, Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom, ya ce takwaransa na Ribas, Nyesom Wike da sauran gwamnonin PDP da suka fusata da zaɓen abokin takarar Atiku ba zasu bar jam’iyyar ba.
Jaridar Leadership ta rahoto Ortom na cewa Wike da sauran gwamnonin da suka fusata sun amince, bayan ganawa a Landan, cewa suna nan daram a jam’iyyar PDP a zaben 2023.
Source:hausalegitng