A Najeriya, yau ake gudanar da zaben shugabanni da kansiloli na yankunan kananan hukumomi shida na Abuja, babban birnin tarayyar kasar.
Hukumar zaben Najeriyar dai ta ce ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka kamata, domin gudanar da zaben, da za a fara kada kuri’a tun daga karfe takwas da rabi na safe zuwa karfe biyu na rana.
Hajiya Zainab Aminu Abubakar, jami’a a hukumar zaben Najeriya, wato INEC, ta shaida wa BBC cewa, za a gudanar da zaben ne a kananan hukumomin da suka hadar da Abaji da AMAC da Bwari da Kwali da Kuje da kuma Gwagwalada.
Jami’ar ta ce, a wadannan kananan hukumomi shida akwai mazabu sittin da takwas da kuma runfunar zabe guda dubu biyu da dari biyu da ashirin da tara.
Hajiya Zainab, ta ce “Tuni aka riga aka raba dukkan muhimman kayayyakin zabe tun cikin daren ranar, wadanda ba muhimmai ba kuma, su tuni aka riga aka raba su, kuma an yi hakan ne domin bayar da damar bude rumfunan zabe a kan lokaci”.
Ta ce, ” Dangane da batun tabbatar da tsaro a rumfunan zabe kuwa, tuni hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar INEC, na aiki tare da jami’an tsaro saboda suma jigo ne a harkar duk wani zabe”.
- Zaben 2023: Ya kamata mulki ya koma kudancin Najeriya bayan Buhari – El-Rufai
- Zaben 2023: PDP za ta karɓe mulkin Najeriya daga Buhari – Bala Mohammed
- Zaben shugabancin jam’iyyar APC ya bar baya da kura a Kano
Jami’ar ta ce kafin zaben sai da aka gudanar da taruka da dama tare da jami’an tsaro, sannan an basu horo tare da daukar isassun jami’an tsaron da zasu sanya idanu a kan kayayyakin zaben da ma yadda zabe ke gudana.
Hajiya Zainab ta ce, jami’an tsaron kuma sun sha alwashin bayar da cikakken tsaron da ya kamata don ayi komai lafiya ba tare da wata matsala ba.
Ta ce, ” Idan mai kada kuri’a ya je rumfar zaben sa za a karbi katinsa sai a tantance shi a tabbatar da cewa a rumfar da yaje zai kada kuri’arsa, daga nan sai ya je ya karbi takardar da zai kada kuri’arsa ya yi zaben”.
Jaimi’ar ta ce, idan har lokaci kammala kada kuri’a ya cika wato karfe biyu da rabi na rana wadanda ke kan layi ba su kada kuri’arsu ba, to za a basu lokaci har sai sun kada kuri’arsu.
Ma’ana dai muddin kana kan layi lokaci ya cika, to ko shakka ba bu zaka kada kuri’arka in ji Hajiya Zainab.