Zababben Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare a yau Talata ya rantsar da kwamitin amsar mulki daga hannun Gwamna Bello Matawalle.
A jawabinsa, Dauda Lawal Dare ya bayyana cewa, an zabo fitatun mutane masu kishin al’umma kuma wadanda su kai wa al’umma hidima don cigabanta a matsayin wadanda za su jagoranci kwamitin amsar mulki.
Dauda Lawal ya kuma kara da cewa, “Wannan aiki ba abu ne mai sauki ba, abu ne mai wahala don barnace ke da saukin yi, don haka sai an taimakawa kwamitin da addu’a don samun nasarar kammala aikinsa cikin wata uku da muka ba shi.
A nasa jawabin Slshugaban kwamitin, MD Abubakar Gusau, ya tabbatar da cewa, za su y kokarinsu wajen sauke nauyin da aka dora musu na ceto rayukan al’ummar Jihar Zamfara.
Abubakar ya kuma tabbatar da cewa za su yi aiki tsakani da Allah kamar yadda su ka yi a gwamnatin da ke ci yanzu, kuma duk wata almundahana za su bayyana ta akan ko waye ba tare d atsoroba ,don Allah ne abun tsoro ba wani dan Adam ba.
Source:LeadershipHausa