Zaɓen 2023; Fitattun ‘yan siyasa da suka sha kaye a zabukan fitar da gwani na APC da PDP.
Zaɓukan da aka gudanar na fitar da gwani na masu neman takara a matakai daban-daban a manyan jam’iyyun siyasar Najeriya biyu a makon jiya, sun bar baya da kura inda wasu ‘yan takara, musamman wadanda suka sha kaye, suka yi zargin tafka magudi.
Kazalika zaɓukan na cike da ruɗani da zarge-zargen tafka kura-kurai da nuna son kai tsakanin ‘yan siyasa da ke fafutukar neman tikitin takara a jam’iyyar APC da ke mulki a kasar da kuma babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
Yanzu dai kusan jam’iyyun sun kammala tsayar da mutanen da suke son yi musu takara, ban da APC da ta dage nata zaɓen na fitar da gwani a matakin shugaban kasa zuwa ranar 6 zuwa 8 ga watan Yuni.
Rahotanni sun nuna cewa akalla sanatocin 14 da ‘yan majalisar wakilai 23 masu-ci ba za su iya komawa kujerunsu ba. Akwai kuma wasu cikinsu da suka samu tikitin gwamna a jihohinsu daban-daban.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege; Sanata Aishatu Dahiru Binani, mai wakiltar Adamawa ta Tsakiya, da Sanata Sandy Onor, sun lashe tikitin neman gwamna na APC da PDP a Delta, Adamawa da Cross Ribas.
Mun yi nazari kan wasu daga cikin fitattun ‘yan siyasa da suka sha kaye a zabukan fitar da gwani na manyan jam’iyyun siyasar kasar biyu, wato APC da PDP:
Kano
Ɗan majalisar da ke wakiltar Kano Municipal, Sha’aban Ibrahim Sharada, ya sha kaye a zaɓen fitar da gwanin neman gwamna a hannun mataimakin gwamna mai-ci, Nasir Yusuf Gawuna.
Hakan ya bai wa tsohon Kwamishinan Ayyuka na musamman, Muntari Ishaq Yakasai damar samun tikitin takarar majalisar wakilai ta tarayya, a karkashin jam’iyya APC.
Akwai tsohon Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmed, da a karon farko shi ma ya shiga takara aka fafata da shi domin neman tikitin wakiltar Gaya/Ajingi/Albasu, sai dai ya sha kaye a hannun dan majalisar da ke kan kujerar, Abdullahi Mahmoud Gaya.
Sannan akwai irin su Barrister Isma’il Ahmed da Sanata Bashir Lado da duk suka sha kaye a zabukan fitar da gwani na APC.
A PDP Kano, akwai Jafar Sani-Bello da ya sha kaye a takarar neman gwamna, inda Mohammed Sani Abacha ya yi nasara.
Sai dai akwai rabuwar kawuna a jam’iyyar PDP reshen jihar Kano domin Sadiq Wali ya fito yana cewa shi ne sahihin dan takarar jam’iyyar a bangaren da Bello Hayatu Gwarzo ke shugabanta.
Jigawa
Sanatoci uku a Jigawa sun sha kaye a neman damar sake komawa kujerunsu a zabukan fidda gwani na jam’iyyar APC.
Biyu daga cikinsu, Sanata Sabo Muhammad Nakudu da ke wakiltar Jigawa ta Tsakiya da Sanata Ibrahim Hassan Hadeja da ke wakiltar arewa maso gabashin Jigawa sun rasa damar samun tikitin gwamna.
Sanatocin biyu sun sha kaye a hannun Malam Umar Namadi da ya yi nasara.
Sanatan da ke wakiltar Arewa maso Yammacin Jigawa, Abdullahi Danladi Sankara ya rasa damar sake komawa kujerarsa bayan ya janye sa’o’i kafin zaben.
Wannan na nufin a yanzu Sanatoci uku daga Jigawa a APC ba za su koma zama majalisa ba a zaben 2023.
Akwai kuma ɗan majalisar wakilai, Muhammad Gudaji Kazaure, da shi ma ya sha kaye a zaben fitar da gwani a yankin Kazaure/Roni/Gwiwa/Yankwashi.
Gudaji Kazaure ya yi rashin nasara ne a hannun Mukhtar Zanna da ke shugabantar karamar hukumar Kazaure.
A PDP, Sale Shehu, tsohon Karamin Ministan Ayyuka, ya sha kaye a hannun Mustapha Lamido, ɗa ga tsohon Gwamna Sule Lamido.
Adamawa
Sanata Aishatu Dahiru da ke wakiltar Adamawa ta Tsakiya ta doke dan majalisar wakilai Honorabul Abdulrazaq Namdas da tsohon shugaban EFCC Nuhu Ribadu wajen samun tikitin takarar gwamnan Jihar.
Komati Laori ya sha kaye neman sake komawa kujerarsa karkashin jam’iyyar PDP domin wakiltar Numan/ Lamurde/ Demsa.
Katsina
‘Yan majalisa takwas a APC da yanzu ke kan kujera sun rasa tikitin sake komawa takara a Katsina, ciki har da ɗa ga ‘yar uwar Shugaba Muhammadu Buhari, Fatuhu Muhammadu da ke wakiltar Daura/Mai’Adua/Sandamu a jam’iyyar APC.
Muhammad ya sha kaye ne a hannun Aminu Jamo wanda ya samu yawan kuri’u 117, Fatuhu kuma ya samu 30.
Hakazalika akwai Murtala Isa, da ke wakiltar Faskari/Sabuwa/Dandume da ya sha kaye a hannun mataimakin kakakin majalisar Jiha, Dalhatu Tafoki.
A Katsina ta Tsakiya, tsohon Kwamishinan Wasanni da Ci gaba, Sani Danlami, ya doke dan majalisa na yanzu, Salisu Isansi.
Haka abin yake a yankin Batagarawa/Rimi/Charanci da Usman Banye ya kada Hamza Dalhatu.
Ashiru Mani da ke wakiltar Mani/Bindawa ya doke Ahmed Yusuf da hana shi sake komawa kujerarsa. Shi ma Ahmed Dayyabu da ke wakiltar Safana/Danmusa/Batsari ya rasa damar komawa kujerarsa bayan shan kaye a hannun Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Abdulkadir Zakka.
Aminu Balele ya kwace tiketin Kurfi/Dutsin Ma. Abdullahi Aliyu ya doke Ahmed Usman Liman da ke kan kujerar a yanzu.
Sokoto
A Sokoto, Sanata Ibrahim Gobir ya sha kaye a takarar neman gwamna a APC.
Rahotanni sun nuna cewa Gwamna Aminu Tambuwal, wanda ya janye domin mara wa tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar baya a zaben fitar da gwani, yanzu haka na hararar kujerar Sanata.
Ana tunanin zai karbi tikitin takarar a hannun Aminu Bala Bodinga wanda ke rike da tikitin a yanzu.
Kogi
Sanata Dino Milaye ya sha kaye a hannun Tajudeen Yusuf da ke wakiltar yankin Kabba-Bunu/Ijumu a majalisar wakilai a PDP, inda yanzu ya rasa takara karkashin PDP ta sake komawa kujerarsa ta Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma.
Sanata mai ci Smart Adeyemi ya rasa damar takarar nemawa kujerarsa domin wakiltar Kogi ta Yamma.
Ya sha kaye ne a hannun Sunday Karimi.
Karimi ya samu kuri’u 288 inda ya doke Adeyemi da sauran mutane hudu da ke takarar a Kabba.