Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da yara dubu 30 ka iya mutuwa sakamakon tsananin yunwa a Arewacin kasar Habasha.
Shugaban Kula da Ayyukan Jin-Kai na Majalisar Dinkin Duniya Mark Lowcock ya ce, tsananin yunwa na ci gaba da karuwa a yankin, bayan da wani bincike ya gano hakan a baya-bayan nan.
Binciken na Majalisar Dinkin Duniya ya gano cewa, mutane dubu 350 ne ke rayuwa cikin mummunan yanayi a yankin Tigray da yaki ya daidaita.
Fadan da aka gwabza tsakanin sojojin gwamnati da na ‘yan tawaye, ya lalata Tigray tare da raba mutane miliyan 1.7 da muhallansu.
Tuni Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF suka bukaci da a dauki matakan gaggawa don magance matsalar.
Binciken dai, gwamnatin Habasha ba ta amince da shi ba, kuma ta musanta cewa akwai yunwa a kasar, yayin da ta nace cewa ana fadada hanyoyin kai kayan agaji yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula.
A shekarar 1984, yankin na Tigray da Wollo sun kasance tamkar wata cibiyar yunwa sakamakon matsalar fari da kuma yaki da ya haifar da mutuwar mutane tsakanin dubu 600 zuwa miliyan guda.
Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce, wani sabon bincike da aka gudanar a Tigray da makwabtan jihohin Amhara da Afar, ya tabbatar da cewa sama da mutane dubu 350 ke cikin bala’i.
Tashe tashen hankula a kananan kasashe yana aukuwa ne sakamakon zaluncin manyan kasashe wadanda basa barin al’ummomin kananan kasashe su zauna lafiya cikin aminci, kamar yadda bincike ya nuna.