Harin da mayakan Boko Haram suka kai garin Gaidam da ke Arewacin Jihar Yobe, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Yobe, ta ce cikin mutane bakwai da suka rasu akwai maza shida da mace daya.
Bugu da kari, yan ta’addar sun kone gidaje tara da shaguna biyu da kuma motoci biyu.
Shugaban Hukumar Ba da Agajin Gaggawa a Jihar ta Yobe (YOSEMA), Dakta Goje Mohammed, ya ce tuni Gwamna Mai Mala Buni, ya ba da umarnin kai agajin gaggawa ga wadanda ibtila’in ya rutsa da su.
Kawo yanzu Hukumar YOSEMA ta kammala kididdigar abubuwan da ya faru kuma Gwamnan Yoben, ya ba da umarnin kai karin kayan agaji.
Kungiyar Ma’aikatan Tashoshin Ruwan Nijeriya (MWUN) sun yanke shawarar janye yajin aikin da suka shirya shiga saboda wasti ka’idojin aiki da kuma rashin doka da wasu kamfanonin mai na kasashen waje da kuma wasu ‘yan kwangila ke yi a harabar tashoshin Ruwan Nijeriya.
Sun yanke shawarar ne bayan da Shugaban Hukumar Tashoshin Ruwan Nijeriya (NPA), Mohammed Bello-Koko, ya shiga tsakanin shugabannin kungiyar ma’aikatan, (MWUN) da kuma wakilan kamfanonin mai na qasashe waje da suke takaddama da kungiyar.
Da yake jawabi ga qungiyar ma’aikata a wurin taron, Mohammed Bello Koko, ya ce, “Za mu yi kokarin tabbatar fahimtar juna da mu’amala cikin mutunta juna don kare ma’aikata shiga yajin aiki, domin tattalin arzikin Nijeriya ba zai iya daukar yajin aikin ma’aikatan tashoshin ruwa ba a halin yanzu, zamu kare duk abin da zai kai ga rufe tashoshin Ruwan Nijeriya a wannan lokacin.”
Bayan taron ne shugaban qungiyar, MWUN, Adewale Adeyanju, ya umarci dukkan ma’aikata su gagauta komawa bakin aiki ba tare da bata lokaci ba.
An kamala taron tare da sanya hannu a takardar yarjejeniya fahimtar juna tsakanin kungiyar kwadago da kuma wakilan kamfanonin da ake takaddama da su.
Source: LEADERSHIPHAUSA