Bashir Machina, halastaccen ‘dan takarar kujerar Sanata a jam’iyyar APC a mazabar Yobe ta Arewa yace nasararsa a kotu daga Allah ne.
A yayin gangamin zagayawa tare da mika godiya ga magoya bayansa, Lawan yace duk wanda zai kare hakkin jama’arsa dole ya ga kalubale
Machina ya dauka alkawarin Tafiya da dukkan kananan hukumomi shida dake karkashin mazabarsa idan ya samu nasara a babban zabe
Bayan makonni da yin nasara a kotu, ‘dan takarar kujerar sanatan Yobe ta arewa, Bashir Machina ya kwatanta nasarar a kotun daukaka kara dake Abuja da ikon Allah, Channels TV ta rahoto.
Machina wanda ya bayyana hakan a Nguru dake jihar Yobe a wata liyafa da gangamin mika godiya ga magoya bayansa, yayi bayanin cewa duk wanda ke yaki domin hakkin mutanensa dole ne ya fuskanci kalubale.
Zaben fidda gwanin da aka yi a ranar 28 ga watan Mayu a Yobe ta arewa a watannin nan ya fuskanci kalubale mai tarin yawa wanda ya kawo hargitsi har aka kai ga danganawa da kotu tsakanin Machina da shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan.
‘Dan takarar sanatan ya sha alwashin tafiya tare da dukkan kananan hukumomi shida dake karkashin mazabarsa idan ya samu nasarar zabe.
Lawan ya kwashe shekaru 20 yana wakiltar mazabarsa ta Yobe ta arewa a majalisar dattawa kafin Machina ya kwace kambunsa tun a zaben fidda gwani.
Bashir Machina yayi nasara a kotun daukaka kara
A wani labari na daban, kotun daukaka kara dake zama a babban birnin tarayya ta jaddada cewa Bashir Sheriff Machina ne halastaccen ‘dan takarar jam’iyyar na kujerar sanatan Yobe ta arewa a jihar Yobe.
Kotun daukaka karar ta aminta da hukuncin wata babbar kotun tarayya dake zama a Damaturu dake jihar Yobe wacce tace shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ba shi ne ‘dan takarar kujerar sanatan Yobe ta arewa ba a zaben shekara mai zuwa.
Kotun ta sanar da cewa, Lawan bai yi zaben fidda gwanin da jam’iyyar APC tayi ba na ranar 28 ga watan Mayun 2022.