Yin Murabus Din Buhari Ba shi Ne Mafita Ga Matsalolin Tsaro Da Kasar Ke Fuskanta Ba.
Wannan yana zuwa ne bayan kira da kungiyar dattawan Arewa ta yi na shugaban mohammadu Buhari ya sauka daga mulki saboda gazawa wajen shawo kan matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta,
Anasa bangaren mai Magana da yawun shugaban Najeriya Garba shehu a cikin wani bayani da ya fitar ya cewa murabus din shugaban kasa daga mulkin kasar ba zai warware matsalar tsaro da kasar ke fuskanta ba.
Yace hukumomin tsaro a kasar suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun shawo kan matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta m usamman a jihohin Kaduna, Nije, da kuma Niger Delta .
Yace kiraye –kirayen da ake ti game da shugaban kasar ya yi murabus daboda rashin tsaro ya isa haka, domin yin murabus dinsa ba shi ne mafita ga matsalolin tsaro da kasar ke fama das hi, wani lamari ne da ya kai kololuwa da ya dade yana sanya damuwa
Daga karshe ya nuna cewa ya kamata alummar kasa su sani cewa gwamnati na bakin kokrinta wajen ganin ta shawo kan matsalar da suke ciki , kuma Yan siyasa su goyi bayan gwamnati wajen ganin an kawo karshen lamarin yadda su ma idan lokacin su ya zo za’a bawu goyon baya.