Yemen na fafata babban yaki ne tsakanin ta da Amurka da ingla
Wani mamba a ofishin siyasa na kungiyar Ansarullah ta kasar Yaman Ali al-Qahum ya bayyana a Yau Talata cewa Yemen na fafata babban yaki da Amurka da Ingila bayan harin da Amurka da Ingila din suka kai musu.
“Masarautarmu da ‘yancin kanmu shine jan layin mu, kuma ba za mu iya lamuntar duk wani zalunci ba.” Wannan wani bangare ne na hirar Ali al-Khoum na yau da tashar Al-Mayadeen ta kasar Labanon.
Yayin da yake ishara da cewa kasar Yemen na fafata babban yaki da Amurka da Ingila saboda keta hurumin Jamhuriyar Yaman da ikonta da kuma al’ummarta ta kowacce fuska, ya jaddada cewa wuce gona da iri kan kasar Yemen ba abu ne mai sauki ba.
Tun da sanyin safiyar ranar 21 ga wata ne Amurka da Birtaniya suka fara kai hare-hare ta sama kan yankuna daban-daban na kasar Yemen, hakan yana biyo bayan matakin da kwamitin sulhu na MDD ya dauka, da nufin matsin lamba kan kasar da kuma dakatar da shingen da sojojin ruwa suka yi wa gwamnatin sahyoniyawa.
An kai wadannan hare-hare ne bayan da dakarun kasar Yemen da ke goyon bayan gwagwarmayar tinkarar al’ummar Palastinu a zirin Gaza, suka kai hari kan wasu jiragen ruwa na yahudawan sahyoniya da suka nufi yankunan da aka mamaye a tekun Bahar Rum da mashigin Bab al-Mandab.
Mamban ofishin siyasa na kungiyar Ansarullah ya jaddada cewa, ba za ta daina taimakawa Falasdinu ba, kuma abubuwan da suke faruwa a Palastinu za su hada kan al’ummar kasar Yemen, da kuma sanya su shiga cikin zanga zanga ta miliyoyin mutane.
Al-Kahhoum ya kara da cewa makircin da ake yi wa dukkanin kasashen Larabawa da na Musulunci yana da girman gaske kuma ‘yan kasar Yemen suna da ilimi mai zurfi da fahimtar irin wannan makircin.