Yau wa’adin ECOWAS kan sojojin Nijar ke cika, mene ne mataki na gaba?
Yayin da wa’adin kwana bakwai da ƙungiyar ECOWAS ta bai wa sojojin da suka ji juyin mulki a Nijar su mayar da mulki ga hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum ke cika, duka ɓangarorin biyu na tsaka mai wuya wajen ɗaukar mataki na gaba kan wannan dambarwa.
A yammacin Lahadin makon jiya ne, shugaban ƙungiyar kuma shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da bai wa sojojin wa’adin kwana bakwai su mayar da ƙasar hannun farar hula ko kuma a ɗauki matakin soji kansu.
Tuni aka ƙaƙabawa sojojin jerin takunkumai, kuma aka yanke masu wutar lantarki da suke samu daga Najeriya, ga rufe masu iyakoki da aka yi, wanda hakan ke nufin ba abin da za a shigar ƙasar su ma ba za su fitar ba.
Yayin da ake ƙara fuskantar matsi ta fuskar siyasa da diflomasiyya, mene ne zai faru tun da wa’adin ya ƙare?
Tsawaita wa’adin za a yi?
Zaɓi ɗaya cikin jerin zaɓukan da shugabannin Ecowas ke da su, shi ne tsawaita wa’adin.
Amma wannan na da haɗari na ci gaba da tsawaita sha’anin, amma duka ɓangarorin za su iya cewa tun da ana ci gaba da tattaunawa ta fuskar diflomasiyya gwara a tsawaita wa’adin.
Matsalar da ake fuskanta a yanzu shi ne aikin shiga tsakanin da Ecowas ke yi za a iya cewa bai yi nasara ba. Wakilcin da aka aika Nijar ɗin daga Najeriya a ranar Alhamis haka suka je suka dawo cikin ƙanƙanin lokaci ba tare da cimma komai ba.
A ɓangare guda kuma su ma sojojin sun ɗauki mataki irin wanda Ecowas ta ɗauka, ta hanyar sanar da yanke hulɗa da Najeriya da Togo da Amurka da kuma Faransa, sannan suka sanar da warware yarjejeniyar soji da ke tsakaninsu da Faransa, wadda ta bai wa uwargijiyar tata damar girke sojinta 1,500 a ƙasar.
Shi kuma Shugaba Bazoum, da ake tsare da shi ya yi amfani da wani kakkausan yare wajen bayyana halin da yake ciki a maƙalar da ya rubuta a jaridar Washigton Post inda yace yana zama ne a matsayin wanda aka yi “garkuwa” da shi.
Hakan ya sa ya nemi taimakon Amurka da sauran ƙasashen duniya domin mayar da ƙasar kan turbar dimokraɗiyya.
A ranar Juma’a Amurka ta sanar da bayar da taimakon da take yi wa gwamnatin Nijar, amma za ta ci gaba da bayar da agajin aminci.
Tsara yadda za a mayar da mulki ga farar hula
Domin sassauta abubuwa da kuma neman maslaha, duka bangaren sojojin Nijar da kuma Ecowas za su iya yarda a zauna a tsara yadda za a miƙa mulki hannun farar hula nan da wani lokaci.
Wanda hakan zai iya haɗa wa ga sakin Shugaba Bazoum da ke hannun sojojin, tare da wasu abokansa na siyasa da aka kama bayan juyin mulki.
Hakan zai iya sassauta wutar da ke ruruwa a zukatan waɗanda suke Allah-wadai da juyin mulki a ko ina suke a Nahiyar Afrika da duniya baki ɗaya.
Kungiyar Ecowas ta amince da tsara yadda za a miƙa mulki ga farar hula a ƙasashen Mali da Burkin Faso da ke makwabtaka da NIjar, waɗanda a baya-bayan nan duka sojoji suke mulka.
Duka tattaunawar da ake yi da su ƙarewa take da matsala, kuma har yanzu aka gaza samun tabbas game da miƙa mulki ga farar hula, a taƙaice ma babu mai tabbacin ko za su miƙa.
Sudan wadda ta ƙirƙiri gwamnatin haɗaka tsakanin sojoji da farar hula a 2019 ita ya kamata ta share hanyar komawar yankin kan dimokraɗiyya bayan juyin mulki, amma sai ta haifar da wani ruɗani.
Kuma a halin da ake ciki na faɗawar ƙasar cikin mummunan rikici tsakanin sojin da ke gaba da juna ya haifar da tsoro a zukatan sojojin da suka yi juyin mulki na daka su yi gwamnatin haɗaka.
Afkawar sojoji
Ecowas ba ta ce za ta yi amfani da sojoji ba idan ba a mayar da Bazoum kan mulki ba, amma ta bar abin a matsayin magana mai harshen damo.
Jami’an Najeriya sun bayyana yanayin a matsayin “zaɓin ƙarshe”.
Shugaba Tinubu ya ce za a iya amfani da soji “domin tursasa sojojin juyin mulki a Nijar matuƙar suka ƙi bin abin da aka umarce su”.
Ecowas ta yi amfani da sojojinta wajen komar da ƙasashe kan tsarin mulki a baya, misali kamar a Gambiya a 2017, lokacin da Yahya Jammeh yaƙi amincewa ya sauka bayan rashin nasara da ya yi a zabe.
Amma yadda za ta yi ruwa da tsaki a yanzu wajen amfani da sojojin a Nijar ya zama wata tsaka mai wuya.
Saboda na Farko, Nijar ce ta fi kowacce ƙasa a yankin Afrika ta yamma faɗin ƙasar, amma idan ka yi la’akari da Gambiya za ka ga wata ‘yan ƙasa ce da ba ta kai ta kawo ba da aka cire daga Senegal, dan haka aika soji cikin Nijar zai bayar da wuya.
Na biyu, Najeriya ta ke da ƙarfi a yankin, wadda ke shigewa gaba wajen amfani da soji a Nijar, itama tana fama da tata matsalar tsaron ta cikin gida, dan haka ta kwashi sojoji masu yawa ta aike Nijar zai zama wata kasada a warinta.
Na uku, daga Burkina Faso har Mali sun ce idan aka aike da sojoji Nijar tamakar an aika musu “goron gayyatar yaki ne” za su zo su kare abokansu da suka yi juyin mulki.
Najeriya da Nijar na da tarihi mai ƙarfi tsakaninsu, ga alaƙarsu mai kyau tamkar dai ‘yan biyu, suna amfani da yare ɗaya na hausa a mafi yawan yankunansu, wanda hakan ba zai bar wasu sojojin Najeriya su yi yaƙin ba idan har ya zo.
Ƙasashe irinsu Aljeriya da ke makwabtaka da Nijar da China da Rasha sun bayar da shawarar ci gaba da amfani da tattaunawa domin lalubo bakin zaren wannan dambarwa.
Bayan wata tattaunawar kwana uku da aka yi a Abuja babban birnin Najeriya babban hafsan sojin Ecowas ya ce sun samar da shirin yadda za a ɗauki matakin soji kan Nijar, yana so Najeriya ta duba kawai.
Najeriya da Ivory Coast da Senegal da Benin sun ce a shirye suke su aike da sojoji idan Ecowas ta amince da afkawar.
A cewar alƙaluman Global Fire Power Najeriya na da sojoji 135,000 yayin da Nijar ke da 10,000 kacal, wanda idan afkawar ta zo ba za ta yi kyau ba, ko shakka babu.
Ko ja babu warware martsalar cikin ruwan sanyi ita ce mafita ga duka ɓangarorin biyu, amma Ecowas a ƙage take ta nuna ikonta tun da ta gaza hana juyin mulki da aka yi a yankin cikin shekara uku da suka gabata.