Yau dan takarar jam’iyyar hamayya ta NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso zai yi zama da Nyesom Wike Da alama Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana neman wanda zai zama abokin takararsa a 2023.
Haduwar Kwankwaso ta yau za ta zo ne sa’anni kadan bayan Peter Obi ya gana da Gwamnan a gidansa.
Mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso zai hadu Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto na musamman cewa Rabiu Musa Kwankwaso yana shirin sa labule da jagoran na jam’iyyar PDP.
‘Dan takaran shugaban kasar zai gana da Gwamnan ne a lokacin da yake neman wanda zai yi masa takarar mataimakin shugabancin kasa.
A halin yanzu Sanata Kwankwaso da jam’iyyarsa ta NNPP su na tsakiyar tattaunawa da ‘dan takarar jam’iyyar LP watau Mista Peter Obi.
An samu tasgaro a tattaunawar yayin da kowane bangare ya dage a kan cewa shi za a ba tikitin shugaban kasa idan jam’iyyun sun hade.
Rahoton ya ce watakila tsohon Gwamnan na Kano zai zauna da Wike ne domin neman wata mafitar idan har ya gaza shawo kan Obi.
Ko bayan banban ‘dan siyasar na Arewacin Najeriya ya sauya-sheka zuwa NNPP, dangantakarsa da Gwamnan na jihar Ribas ba ta cabe ba.
‘Ya ‘yan jam’iyyar hamayya ta PDP na reshen jihar Kano duk sun zabi Wike ne a lokacin zaben fitar da gwanin zama shugaban kasa a PDP.
Har yanzu NNPP ba ta tsaida takamaimen ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa ba, babu mamamki Wike yana cikin lissafin da ake yi.
Wike ya tada hankalin PDP Ku na da labari cewa shugabannin PDP da Atiku Abubakar sun fara jin tsoron Nyesom Wike ya tsallaka zuwa wata jam’iyyar kafin zabe.
Da alama Nyesom Wike ya sa ran Atiku Abubakar zai dauke shi a matsayin abokin takara a PDP, don haka aka tura kwamiti ya ba shi hakuri.