Yaron tsohon gwamna , okunbo Ajasin ya jagoranci zanga-zangar da mutane suka shirya a farkon makon nan a Ibadan
Wannan matashi yana cikin ‘ya ‘yan tsohon gwamnan jihar Ondo, Marigayi PA Adekunle Ajasin Ajasin yake cewa akwai bukatar Yarbawa su tashi domin su kare kansu daga harin ‘yan ta’adda.
Kayi musharaka a wannan shirin na Patreon, mu hada kai wajen canza rayukan mutane! Oyo.
Tokunbo Ajasin wanda yaron marigayi Cif Adekunle Ajasin ya shiga zanga-zangar da aka shirya a ranar Litinin din da ta wuce.
Daily Trust ta kawo rahoto an ga Tokunbo Ajasin wajen zanga-zangar da matasa da dattawa mazauna garin Ibadan, jihar Oyo suka yi a farkon makon nan. Micheal Adekunle Ajasin ya yi gwamna a tsohuwar jihar Ondo na shekaru hudu a jam’iyyar UPN.
‘Dan siyasar ya rasu ne tun a shekarar 1997 yana shekara.
Ibo sun buɗa wuta, sun ce bai dace Atiku ya dauki Wike a Jam’iyyar PDP ba Watakila Ajasin yana cikin daula, amma wannan bai hana shi fita kan titi domin jawo hankalin hukuma da mutane a kan irin abubuwan da su ke faruwa ba.
Masu zanga-zangar sun bukaci kawo karshen matsalar tsaro da ake fama da ita a kudu maso yamma.
Tokunbo Ajasin ya jagoranci jama’a a wannan zanga-zangar lumanar da aka shirya a garin Ibadan, su na dauke da rubutu da za su ankarar da gwamnati.
Baya ga haka, wasu masu zanga-zangar sun cika titunan babban birnin jihar Oyo na Ibadan, su na masu yin kira ga al’umma da su shirya kare kansu da kansu.
Dalilin yin zanga-zangar shi ne ganin hallaka mutane da ake yi babu gaira babu dalili da garkuwa da mutane da fyaden da ake fama da shi a jihohin Yarbawa.
Masu zanga-zangar sun ce kashe Bayin Allah da aka yi a cocin St Francis Catholic Church da ke garin Owo a jihar Ondo ba shi ne farko da aka yi a yankin ba. Kamar yadda rahoton ya bayyana, masu zanga-zangar sun yi ikirarin ‘ya ta’adda sun taba kai irin wannan mugun hari a Igangan a garin Ibarapa da ke jihar Oyo.
A rahoto daga Punch, an ji Steve Abioye mai kare hakkin Yarbawa yana irin wannan kira. Alabi Arogunmasa mai shekara 75 ya nemi matasa su tashi tsaye.
Gwamnatin El-Rufai Dazu an ji cewa Malam Nasir El-Rufai ya yi abin da ba a taba gani ba a tarihin Kaduna, ya nada mace a matsayin kwamishinan kananan hukumomi na jihar.
Watakila a Najeriya babu jihar da maza ba su fi mata yawa a majalisar zartarwa ba, amma a jihar Kaduna, mata tara ne kwamishononi, maza kuma su takwas.