Yariman masarautar Sokoto, Alhaji Shehu Malami, ya rasu yana da shekaru 85 a duniya a birnin Cairo dake kasar Misra.
Takardar da mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya fitar ce ta tabbatar da mutuwarsa a ranar Litinin.
Shugaba Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga abokai, ‘yan uwa, masarauta, gwamnati da jama’ar jihar Sokoto kan wannan babban rashin.
Yariman Sokoto kuma ‘dan kasuwa, Alhaji Shehu Malami, ya kwanta dama. Ya rasu jiya Litinin a birnin Cairo dake kasar Misra yana da shekaru 85 a duniya.
Takardar da mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, ya fitar ita ta tabbatar da mutuwarsa.
Shehu yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwatanta mutuwar Yariman Sokoton kuma ‘dan kasuwa, Alhaji Shehu Malami Yariman Sokoto, da abun takaici da bada mamaki.
Yace shugaban kasan yayi martani kan mutuwar tsohon Sarkin Sudan na Wurno da aka sanar masa a garin Cairo dake Misra.
“Wannan lamari ne mai bada mamaki da takaici. A gaskiya na girgiza da jin shi. Wannan tunatarwa ce ta yadda rayuwa take babu tabbas. ”
Babban ‘dan kasuwa ne wanda ake mutuntawa a duniya, wanda ya yadda da karfin tattalin arzikin kasar nan.
Madubin dubawa ne a kasuwanci, masana’antu da kuma fannin gargajiya.
“Mutuwarsa babban rashi ce ga kasar
Ina mika ta’aziyya ga ‘yan uwansa da abokai, masarautar da gwamnati tare da jama’ar jihar Sokoto. Allah yasa ya huta.” – Shugaban kasan yace.
Malami wanda tsohon babban kwamishinan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu, yana zama tare da iyalansa ne a kasar Misra.
Malami babban ‘dan kasuwa ne wanda ya taka rawar gani wurin cigaban wasu bankunan ‘yan kasuwa a Najeriya da wasu manyan kamfanoni a kasar nan, The Cable ta rahoto.
A wani labari na daban, wani ‘dan majalisar jiha mai wakiltar mazabar Lere ta jihar Kaduna ya kwanta dama.
Suleiman Aliyu ya rasu yana da shekaru 53 a duniya bayan jinyar rashin lafiyar da yayi fama da ita a asibitin Barau Dikko da ke cikin garin Kaduna.
Ya rasu ne bayan kwanaki kadan da kotu ta tabbatar da shi wanda ya ci zaben mazabar Lere a zaben 2019.