Sabani ya turnike auren yar gidan gwamnan Kano da mijinta kan rabuwar su a auratayya da suka shafe shekaru 16.
Asiya Balaraba ta maka mijinta a kotu kan ya bada damar a rabata da mijin nata mai suna Inuwa Uba.
Alkalin kotun shari’ar muslunci da ke zamanta a kano ya umarci ‘yan jarida da su basu wuri dimin tattauna shari’ar a asirce.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa yar gidan ganduje ta nemi da kotu ta raba aurensu da mijinta (Cikin Lumana) wanda ya shafe tsawon shekaru 16 ita da mijinta Inuwa Uba, tana mai ikirarin shan wuya a gidan auren.
Amma mijin ya tubure kan cewa yana son matarsa sannan ya bukaci kotu ta bar wannan batun, kuma ta basu lokaci su tattauna a tsakaninsu, ko hakan zai sa ta canja ra’ayi.
Mai shari’a Abdullahi Halliru ya bukaci da ‘yan jaridu da su basu waje a kotu domin su tattauna batun sakin da yar gidan gwamnan Asiya ta shigar kan raba aurensu da mijinta.
Alkalin yace “wannan batu ne da kowa zai iya gani musanman ma da ya shafi auratayya, amma wannan na musamman ne, dan haka muna bukatar da yan jarida su bamu waje, sabida tattauna batun a cikin sulhu.”
Daganan kuma alkalin ya fara saurarar shari’ar a asirce a ofishinsa.
Yayin da yake yanke hukunci, Alkalin kotun ya bawa mijin sati biyu kan yaje ya tattauna da matarsa kafin yanke hukuncin. Dan haka alkalin ya basu biyar ga watan Janarun sabuwar shekara kan su dawo.
Mai Ya Janyo Zasu Rabu
Jariadar Daily Nigerian ta tattaro cewa a shekarun baya ‘yar gidan gwamnan ta samu sabani da ahlinta sabida yadda ta gooyi bayan mijinta.
Yayin da ahlin nata na ganin mijin ya gaje mata dukiyarta
Wata Majiyar sirri ta fadawa jaridar cewa lokacin da Asiya ta canja ra’ayinta kan mijin nata, an tura jami’an tsaro da makamai zuwa gidan mijin, inda suka balle kofar gidan suka shiga su kai awon gaba da wasu takardu masu muhimmanci na shi mijin.
Takardun da ake tunanin sun dauka sun hada da takardun kamfanin shinkafarsa na Zari’a Road, da wasu na gidajen mansa da dai sauransu.
Source:LegitHausa