Yanzunan Kotu ta hana a saki Abba Kyari.
Mai Shari’a Inyang Eden Ekwo na kotun tarayya dake Abuja ya nemi a ci gaba da tsare dansanda DCP Abba Kyari da ake zargi da safarar gwaya.Abba Kyari ne dai ya kai gwamnatin tarayya kotu inda yake neman a bada belinsa saidai kotun ta ki amince masa.
Kyari ta hannun lauyansa, Cynthia Obianuju Ikena yace yana fama da matsanancin ciwon siga wanda yace a bada belinsa dan ya je ya nemi magani.
Yacs ciwon yana wa rayuwarsa barazana.
Kotun tace sai ta ji daga bakin gwamnatin tarayya tukuna kamin ta duba yiyuwar bayar da belin Abba Kyari.
Kotun ta sanya ranar 24 ga watan Fabrairu dan ci gaba da sauraren shari’ar.