Yanzu Yanzu: Yan daba sun tarwatsa zanga-zangar NLC da ke gudana a Kaduna
Wasu ‘Yan daba da aka yo haya sun tarwatsa zanga-zangar lumana da kungiyar kwadagon Najeriya (NLC) ta fara a jihar Kaduna, jaridar Daily Trust ta ruwaito, yanzu
A yayin da zanga-zangar ke gudana, sai wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka shigo wajen a motoci biyu da adaidaita sahu inda suka fara jifan masu zanga-zangar. Wasu daga cikin maharan sun rufe fuskokinsu dauke da wukake da sanduna.
“Sun zo ne a cikin mota suka fara jifan ma’aikatan da ke zanga-zangar. Sai mutane sun fara gudu amma ma’aikatan sun sami damar korarsu, ” wani ganau ya shaida wa jaridar.
Channels TV ta kuma ruwaito cewa Ma’aikatan sun hallara a sanannen hanyar shataletale na NEPA da ke cikin babban birnin na Kaduna don ci gaba da zanga-zangar su a rana ta biyu lokacin da yan daban suka mamaye yankin suka fara jifan su da duwatsu da wasu muggan makamai.
A wani labarin na daban An Dawo da £4.2m Zuwa Najeriya, Kudaden Da Ibori Ya Sace.
Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya tabbatar da cewa.
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta karbi £4,214,017.66 na almundahanar da ke da alaka dangin tsohon Gwamnan Jihar Delta, James Ibori.
Umar Gwandu, mai taimakawa na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, ofishin Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja ranar Talata, in ji Channels Tv.
A cewar sanarwar an sanya kudin a cikin asusun da aka ware na Gwamnatin Tarayya tare da darajar Naira daidai da kudin ya zuwa 10 ga Mayu, 2021.
Mista Malami ya sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna don dawo da dukiyar da Ibori ya sace zuwa gida Najeriya a madadin Gwamnatin Tarayyar Najeriya.
Daily Trust ta ce Gwamnatin jihar Delta ta yi zanga-zangar cewa ya kamata a mayar da kudin zuwa jiharta. Karin bayani nan gaba…