A halin yanzu dai shugaba Bola Tinubu yana ganawa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwakwaso.
Idan za a tuna cewa tsohon gwamnan Jihar Kano ya zo na hudu a zaben shugaban kasa da ya gabata.
A cikin kwanaki biyun da suka gabata shugaban ya gana da gwamnonin adawa.
A baya shugaba Tinubu ya gana da Kwankwaso a kasar Faransa, inda wasu majiyoyi suka ce ya yi wa tsohon gwamnan na Kano tayin kujerun minista guda biyu.
Sai dai waccar ganawar tasu ba ta yi wa wasu jiga-jigan jam’iyyar APC dadi ba.
A wani labarin na daban shahararren dan wasan Nigeriya, Bictor Osimhen ya zama dan wasa daga nahiyar Afirka na farko da ya lashe kyautar gwarzon dan wasan da yafi kowa zura kwallo a raga a gasar Siriya A ta kasar Italy.
Dan wasan, mai shekaru 26 wanda yake buga wasa a kungiyar Napoli ya zura kwallaye 26 a kakar wasan da aka kammala a kasar.
Osimhen ya taimaka wa Napoli ta lashe gasar Siriya a karon farko cikin shekaru 30 kuma yana daya daga cikin matasan ‘yan wasan da tauraruwar su take haska wa a yanzu.
Har ila yau, dan wasan ya kasance gwarzon dan wasan Siriya A a wannan kakar.
Tuni kungiyoyin Manchester United da Chelsea da Real Madrid suka fara zawarcin dan wasan wanda ake ganin zai iya komawa daya daga cikin manyan kungiyoyin nahiyar turai.