Labarin da yake zuwa mana yanzu da dumi dumi shine a kaduna ta wanke jagoran mabiya mazhabar shi’a na afirka Allama sheikh ibrahim yaqoob zakzaky H.
Kotun dai ta tabbatar da cewa malamin bai aikata laifin komi ba shi da mai dakin sa saboda haka yanzu yayi firi.
Kamar yadda majiyar mu ta tabbatar mana yanzu dai almajiran malamin sun fara bayyana farin cikin su bisa wannan nasara da aka samu da kuma ‘yancin da jagoran sya samu bayan shafe fiye da shekara biyar yana tsare ba bisa ka’ida ba a hannun gwamnati.
Shari’ar da aka jima ana fafatawa dai yanzu tazo karshe kuma gaskiya tayi halin wanda hakan yake nuna karfin bangaren shari’a najeriya.
Idan dai ba’a mance ba gwamnatin najeriya tana tsare da malam zakzaky ne tun shekaru fiye da biyar da suka gabata bisa zarge zarge da tuhume tuhume wadanda tuni shehin malamin ya musan ta inda ya kira tuhume tuhumen a matsayin rubbish and nonesence kuma a matsayin cin zarafin shaksiyyar sa.
Wata babbar kotu ma a abuja ta taba wanke shehin malamin sai yau kuma 28 ga wajan yuli wata kotun a jihar kaduna itama ta saki malamin kuma ta wanke shi daga dukkan laifukan da aka tuhume shio dasu a da.
Babban labari ana sa ran dai abinda shehin malamin zai farayi bayan wanke shi da kotun tayi shine tafiya domin neman lafiya, kamar yadda aka sani shehin malamin yana fama da matsananciyar cuta sakamakon harsasai masu guba da sojojin najeriya sukayi amfani das a kansa lokacin kaddamar da hadisar zariya wacce tayi sanadin kisar mutane fiye da dubu ciki har da ‘ya;’yan malamin uku, dadi kan wasu uku da aka taba kashe masa.
Masu lura da lamurran siyasa sun tabbatar sheikh zakzaky shine wanda aka fi zalunta a wannan karnin a najeriya.
Zamu kawo muku cikakken labari nan gaba kadan