Mai shari’a Ladiean Akintola na babbar kotun Oyo ya hana hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da babban lauyan gwamnatin tarayya kamawa, bincika, tursasawa, da toshe asusun banki na Cif Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho, yanzu The Nation ta ruwaito.
An bayar da wannan umurnin ne bayan wani tsohon kudiri da lauyansa Cif Yomi Aliu (SAN) ya gabatar a kotun a ranar Laraba.
Wannan ya samo asali ne daga kudirin neman diyyar Naira biliyan 500 saboda mamaye gidansa da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ranar 1 ga watan Yuli.
Aliu ya bayyana kwarin gwiwa cewa AGF Abubakar Malami (SAN) ba zai yi watsi da umarnin kotu ba, yana mai jaddada cewa an bayar da umarnin ne kai tsaye kan ofishinsa. An dage sauraren karar zuwa 18 ga watan Agusta. Karin bayani na nan tafe.
A wani labarin na daban mai kama da wannan Yanzu-Yanzu DSS sun bi umarnin kotu, sun gabatar da dukkan hadiman sunday igboho a kotu.
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gabatar da gaba ɗaya hadiman Sunday Igboho a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja ranar Laraba, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
Wannan yazo ne kasa da awanni 72 bayan kotu ta baiwa hukumar umarnin ta gabatar da baki ɗaya makusantan jagoran yan awaren kafa kasar yarbawa.
A zaman kotun na ranar Litinin, DSS ta gabatar da mutum takwas ne kacal a gaban kotun.
Sunday igoho wanda ke zaman dan rajin ballewa daga tarayyar najeriya gami kafa kasar yarabawa mai cin gashin kanta ya tsere daga najeriya ne bayan da hukumar DSS suka kai wani harin ba sani ba sabo.
Rahotanni sun tabbatar da cewa sunday igoho ya fece ne zuwa makociyar kasar Benin a yayin da jami’an tsaron na najeriya suke cigaba da farautar sa domin gurfanar da shi gaban kuliya.