Jami’an rundunar ‘yansanda sun kama wani da ake zargi kuma ake nema ruwa a jallo kan aikata miyagun laifuka da suka hada da safarar makamai da kayan abinci; kai rahoton sirri ga tawagar masu garkuwa da mutane da ke addabar babban birnin tarayya Abuja da kewaye.
Wanda ake zargin mai suna Mohammed Hamza (Auta) mai shekaru 25, rundunar da ke yaki da masu garkuwa da mutane ce ta kama shi a dajin Mongoro da ke kan iyaka da Jihar Neja.
Kakakin rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ta ce, wanda ake zargin ya dade da kasance cikin jerin sunayen wadanda rundunar ke nema ruwa a jallo, ana zarginshi ne da hannu wajen samar da bindigogi, alburusai da sauran makamai; kayan abinci da haramtattun kwayoyi ga ‘yan bindiga a maboyarsu daban-daban a cikin dazuzzuka ta hanyar amfani da babur.
Ta ce, rundunar ta kwato bindiga kirar AK47 guda daya, harsashan AK47, wayar hannu daya, kayan abinci da kuma babur wanda ba a yiwa rajista ba a hannun wanda ake zargin (Auta).
A wani labarin na daban ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta Tarayya, a ranar Litinin, ta fadakar da jama’a game da yin taka tsantsan yayin da Arewacin Ghana da kan iyakar kasar Burkina Faso da Togo aka rahoto barkewar cutar Anthrax.
Anthrax cuta ce wacce da farko take shafar dabbobi amma takan iya yaduwa zuwa ga mutane ta hanyar hulda da dabbobin da suka kamu da cutar. Kamar shafar fata, cin nama ko shan nonon dabbar da ta kamu da cutar.
Sai dai, an bayyana cewa, Anthrax ba mai yaduwa ba ce a iska, ana iya kamuwa da ita ta hanyar mu’amala da wadanda suka kamu da kwayoyin cutar ne kawai.
Anthrax tana iya bayyana ta nau’i-nau’i daban-daban, ciki har da alamu masu kama da mura kamar tari, zazzabi, ciwon tsoka sannan kuma, idan ba a gano cutar da wuri an magance ta da wuri ba, zata iya haifar da ciwon huhu mai tsanani wacce za ta iya toshe numfashi ta kai ga mutuwa.
A cewar wata sanarwa da babban sakatare a ma’aikatar, Dr Ernest Umakhihe ya fitar; Jihohin Sokoto da Kebbi da Neja da Kwara da Oyo da Ogun da kuma Legas sun fi fuskantar hadari sabida kusancinsu da Burkina Faso da Togo da Ghana, don haka, ana bukatar a kara kaimi wurin yin allurar rigakafin dabbobi a wadannan jihohin dama daukacin jihohin tarayyar Nijeriya.