‘Yansanda sun gayyaci fasto Adelana Solomon da yace ya hango Bola Tinubu ba zai zama shugaban Najeriya ba.
Faston ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda kuma yace idan har Tinubu ya zama shugaban kasa to mutuwa zai yi kamin ya kammala wa’adinsa na shekaru 4 akan mulki.
Hakanan kuma faston ya caccaki gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda yace bai iya mulki ba.
Saidai Tuni ‘yan sanda suka gayyaceshi ya je ya amsa tambayoyi.
Read more : ‘Yan Sandan Isra’ila Sun Ruguza Gidan Wasu Iyalai A Sheikh Jarrah