Kamar yadda wakilin mu na yankin pambeguwa ya tabbatar mana, ‘yan uwa almajiran sheikh Ibrahim Yaqoob Alzakzaky na yankin pambeguwa wanda ya hada da birnin jos sun fara gudanar da tattakin bana shekarar 2021 cikin nasara.
Wakilin ‘yan uwa na garin jos malam adamu tsoho jos ne ke jagorantar tattakin na yankin pambeguwa wanda aka soma cikin tsri gami da bin tsare tsare tsaren da masu shirya tattakin suka tsara.
Yankin pambeguwa na cikinmanyan yankunan da ake gudanar da wannan babbar kuma muhimmiyar ibada ta tattaki duk shekara kuma wannan shekarar ma ‘yan uwan na yankin pambeguwa basuyi kasa a gwuiwa ba sun shirya tattakin kuma ga dukkan alami kwalliya tana biyan kudin sabulu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa tattakin ya samu tarba mai kyau daga al’ummar gari, inda suke yabawa gami da sa albarka kuma suna fatan ayi lafiya kuma a kammala a dawo gidalafiya.
Tattakin dai ana shirya shi ne duk shekara a fadin garuruwan najeriya dama makotan ta domin tunawa da ranar arba’in na kisan jikan manzon Allah (S), Imam Hussain (s.a).
A lokaci guda kuma tattakin na zaman tunawa da yadda aka ja iyakan gidan annabta tun daga karbala har zuwa birnin dumaishq na siriya a kafa, babu takalma kuma cikin tsananin kishirrwa, yunwa da gajiya.
Ana tabbatar da cewa a iya cikin najeriya a kalla masu tattaki sun kai miliyoyi, wadanda sukan kwararon daga garuruwa mabambanta domin musharaka a wannan ibada wacce daga shekara sai shekara.
Ana sa ran sauran yankuna ma zasu gudanar da irin wannan tattaki musamman yankin kano wanda rahotanni suka tabbatar da cewa suma yau sun fara tattakin nasu, kuma abin yana bada sha’awa musamman ga mutanen gari masu dafifi domin kallon masu tattakin tare da nuna sha’awar su.
Muna sa ran kawo muku rahoton tattakin na kano da damar hakan ta samu, ku dai ku ksance da jaridar Nigeria21.com a kowanne lokaci.