Tashin hankali a Abuja yayin da wasu miyagun yan bindiga sun kashe mutum biyu sannan suka yi awon gaba da manoma 13 a yankin babban birnin tarayya Abuja.
Bayanai sun nuna cewa maharan sun kutsa har cikin gida suka sace mutane a ƙauyen Rafin Daji, daga bisani suka wuce Kutara.
Kakakin hukumar yan sanda bata amsa sakonnin karta kwanan da aka aike mata game da sabon harin ba.
‘Yan bindiga sun ci karensu babu babbaka ranar Asabar da misalin ƙarfe 11:00 na dare a kauyukan Rafin Daji da Kutara dake gundumar Gurdi, ƙaramar hukumar Abaji, birnin Abuja.
Yayin wannan sabon farmakin tsahin hankalin, ‘yan ta’addan sun kashe mazauna ƙauye biyu, sannan suka yi awon gaba da wasu manoma 13.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwanaki Tara da suka gabata, ‘yan bindiga sun kai farmaki ƙauyukan Gasakpa da Mawogi dake gundumar Gawu, duk a ƙaramar hukumar Abaji, inda suka yi garkuwa da manoma Takwas.
A Jihar Borno Wani ɗan uwan mutanen da harin ranar Asabar ya shafa a Rafin Daji, Shu’aibu Ɗantani, yace yan bindiga sun tafka ta’asarsu babu tirjiya, suka buɗe wuta don tsorata mutane.
A cewarsa, maharan sun kutsa cikin gidaje huɗu, suka tattara manoman suka yi awon gaba da su zuwa wani wuri da babu wanda ya sani.
Bugu da ƙari, Ɗantani yace yan bindigan sun zarce zuwa ƙauyen Kutara dake makwaftaka da su, suka hallaka mutum biyu, daga bisani suka ɗauki miji da mata a ɗakin kwanansu.
Magajin garin Gulida a gundumar Gurdi, Sadauna Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar ta wayar salula.
Yayin da aka tuntuɓi mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan Abuja, DSP Adeh Josephine, ba ta maida sakon karta kwanan da aka tura mata game da sabon harin garkuwa da mutanen ba.
A wani labarin tashin hankali kuma kuma ‘Yan Bindiga Sun Kwashi Kashinsu a Hannun Yan Sanda Yayin da Suka Yi Yunkurin Sace Dan Takarar PDP.
Gwaraazan jami’an yan sanda a jihar Katsina sun kubutar da ɗan takarar kujerar majalisar jiha karkashin inuwar PDP a Kankiya.
Mai magana da yawun yan sanda, SP Gambo Isah, ya tabbatar da nasarar bayan gumurzu da maharan da daren Asabar.
Source: LEGITHAUSA