‘Yan uwa almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky wadanda ak fin sani da ‘yan shi’a, a wani sakon da suka fitar ranar asabar sun bayyana yadda wasu gungun wahabiyawa da magoya bayan su suka kai hari masallachin su mai suna Hussainiya, a unguwar dorayi babba dake jihar kano.
A wani bayani wanda wani mai suna sulaiman gambo ya sanyawa hannu ya bayyana harin a matsayin yunkurin haddasa rikici tsakanin shi’a da sunnah a birnin kano.
Hussainiyar Almujtaba wacce take a dorayi babba dake birnin Kano, karamar hukumar Gwale, cibiyar addinin musulunci ce wacce almajiran Malam Ibrahim Zakzaky suke gudanar da ayyukan su na ibadar bautar Allah ta’ala a yanayin lumana da kwanciyar hankali.
Amma a ranar juma’a 28/8/2022 na yamma muna shirin fara tarukan mu kamar yadda muka saba sai muka lura wasu bata gari sun haura ta katangar baya kuma sun banka wuta abinda ya sabbaba asarar kayan da kimar su bata gaza milyan 3 ba.
Mun sanar da DPO na dorayi babba kuma yazo da kansa tare da yaran sa ya duba abinda faru.
Sanannen abu ne cewa tun shekarar 2021 wasu marasa son zama lafiya ke kokarin hana mu damar da doka ta bamu na aiwatar da ayyukan addini bisa abinda muka yadda dashi saboda mun saba da akidar su.
Wa’azin tada hankali da akayi a masallacin juma’a shine muke zargin ya haddasaa wannan abin takaici.
Mun rubuta cikakkaken korafi zuwa ga hukumar ‘yan sanda kuma ko a ranar juma’a ma sai da aka samu wasu bata gari suka kawo mana hari muna tsaka da taron mu na zaman lafiya.
Tuni muka shirya zama da hakimin Gwale domin sanar dashi halin da ake ciki.
Muna kira ga al’umma dasu rungumi zaman lafiya, su kuma wahabiyawa muna kira garesu da cewa dole suyi hakuri da fahimtar mu kamar yadda mukayi hakuri suke aiwatar da tasu bamu tsangwame su ba.