Jaruman yan sanda a Jihar Nasarawa sunyi nasarar kama daya cikin fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Kuje a Abuja.
An kama, wanda ake zargi dan Boko Haram ne, Hassan Hassan a karamar hukumar Keffi ta Jihar Nasarawa yana kokarin tserewa Mai magana da yawun yan sandan Jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel, ne ya tabbatarwa manema labarai hakan a Lafia.
Biyo bayan harin da aka kai a gidan yarin Kuje da ke Abuja a baya-bayan nan tare da tserewar fursunoni, Rundunar yan sandan Nasarawa ta ce ta kama wani Hassan Hassan, wanda sunansa da hotonsa ke cikin fursunoni da aka ce sun tsere cikin wadanda ake zargin yan Boko Garam ne a karamar hukumar Keffi.
Mai magana da yawun yan sandan Jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Lafia, ranar Asabar, The Punch ta rahoto.
Ya ce: “Dakarun jami’an yan sandan ne suka kama wanda ake zargin dan Boko Haram ne da ya tsere a karamar hukumar Keffi na Jihar.
“Kwamishinan yan sanda, CP Adesina Soyemi, ya bada umurnin a kai wanda ake zargin wani wuri mai tsaro yayin da ake cigaba da neman sauran wadanda suka gudun domin mika su ga hukumar da ta dace. ”
CP Soyemi ya gode wa jami’an yan sandan saboda jajircewa ya kuma bawa al’umma tabbacin rundunar za ta cigaba da kokarin samar da tsaro ga kowa.”
A wani labarin na daban a wata sanarwa da babban sakataren JNI, Dakta Khalid Abubakar Aliyu, ya fitar ranar Alhamis a Kaduna, Amirul Muminin ya kuma bukaci alhazan Nijeriya da su yi wa Nijeriya da shugabanninta addu’a na musamman, yayin da suke tsaye a kan dutsen Arafat.
Sanarwar ta kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su nemi taimakon Allah domin samun kwanciyar hankali, tsaro da zaman lafiya da ci gaban Nijeriya a daidai lokacin da babban zaben shekarar 2023 ke gabatowa.
JNI, ta sake nanata bukatar yin addu’o’i sosai domin samun sauye-sauyen siyasa cikin lumana, da kuma kawo karshen kalubalen zamantakewa da tattalin arziki iri-iri a kasar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Idan aka yi la’akari da cewa al’amura guda biyu suna haduwa a ranar Juma’a, wato gobe akwai bukatar tunatar da musulmi da su yi azumin ranar 9 ga watan Zul-Hijja (Arafat), kamar yadda Annabi (SAW) ya koyar da shi. kasancewarta rana ta musamman ta Juma’a kuma ita ce mafificiyar ranar mako, a cikinta ake yin Sallar Juma’a da amsa addu’o’i a cikin sa’a ta musamman da Arafat – mafi kyawun ranar shekara a cikinta.
Allah mai rahama yana gafartawa bayinsa kuma yana amsa dukkan addu’o’in ranar Arafat.