Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara, ta tabbatar da kubutar da wasu ‘yan salin ƙaramar hukumar Rijau, su bakwai da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su. ‘Yan sandan sun ce bayan samun bayanan sirri, suka ƙaddamar da atisayen haɗin guiwa da jami’an sojin Najeriya a cikin dajin Ɗan Sadau dake ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara, a ranar 25 ga watan Fabarairun wannan shekara. Inda suka yi nasarar kubutar da waɗanda aka yi garkuwa da sun. Kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar SP Mohammed Shehu (NIPR) ya tabbatar.
Bayan kubutar da waɗanda aka sacen, rundunar da garzaya da su, zuwa asibitin ƙwararru na Yariman Bakura dake garin Gusau, domin duba lafiyar su. Rundunar ta kuma ce, da zarar ta kammala bincike, za ta miƙa su ga kwamishinan ‘yan sandar Jihar Neja, domin hannanta su ga iyalan su.
Waɗanda aka kubutar ɗin dai sun shaida cewar, an yi garkuwa da su ne, a ƙauyen Chibade dake ƙaramar hukumar Rijau, a ranar 21 ga watan Fabarairun wannan shekara, a yayin da ‘yan bindigar suka kai hari a yankin. Waɗanda ‘yan ta’addan suka kai su dajin na Ɗan Sadau.
Comrade-Zakari Y. Adamu Kontagora