‘Yan sanda sun kashe masu safarar makamai biyu a Zamfara
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce jami’anta sun kashe wasu masu safarar makamai biyu a kan hanyar Gummi zuwa Anka.
Bayan sun yi musayar wuta na kusan sa’o’i da masu safarar makaman, waɗanda ake zargin sun ɗauko makaman tun daga jihar Taraba domin kai su sansanin ‘yan ta’adda a Zamfara.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Mohammed Shehu Anipr, ya sanya wa hannu, ya ce lamarin ya faru ne bayan da jami’an nasu suka samu bayanan sirri game da mutanen waɗanda ke cikin ƙaramar mota ƙirar ‘Toyota Corolla’ ɗauke da muggan makamai domin kai su sansanin ‘yan ta’adda a jihar.
Bayan musayar wutar ‘yan sandan sun kama mutum biyu waɗanda suka ji munanan raunuka yayin da wasu suka tsere da raunkan harbi a jikinsu.
An kai mutanen biyu asibiti inda daga baya likita ya tabbatar da cewa sun mutu bayan an kwantar da su a asibitin.
Daga cikin abubuwan da ‘yan sandan suka ƙwato sun haɗar da ƙaramar mota kirar Toyota Corolla, da harsasan manyan bindigogin harba gurneti uku, da abubuwan fashewa uku, da harsasan bindiga ƙirar AK47 151, da harsasan makamin harbo jirgin sama 200, da wasu layu da guraye.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Kolo Yusuf ya sake jadadda burin rundunar na fatattakar ‘yan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuka daga jihar, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin jihar.