‘Yan sanda sun kama wani mutum bisa zargin sayar da ‘ya’yansa uku
Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya ta kama wani mutum bisa zarginsa da sayar da ‘ya’yansa guda uku.
Yayin da ‘yan sanda ke holen mutumin a ofishinsu da ke unguwar tsohuwar GRA a jihar, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Grace Iringe-Koko, ta ce sun kama mutane masu yawa da ke harkar sayar da ƙanana yara a fadin jihar.
Mutumin mai suna Michael Charles, ya amince cewa ya sayar da ‘ya’yansa, yana mai cewa talauci da rashin halin ɗaukar nauyin ‘ya’yan nasa ne ya sanya shi ɗaukar matakin.
Sauran mutanen da ke da hannu wajen sayar da yaran sun hadar da wani likita da kuma wani tsohon kansila.
Yayin da take magana a madadin mahaifiyar yaran wadda ita kurma ce, kakar yaran ta ce surukin nata ya daɗe yana sayar da ‘ya’yan da ‘yar tata ke haifa, tare da yi mata ƙaryar cewa yaran mutuwa suke yi a lokacin haihuwarsu a asibiti.
Sanarwar da ‘yan sanda suka fitar, na cewa bayanan da suka samu sakamakon kama wasu da ake zargi da safarar ƙananan yara ne ya kai su ga gano waɗannan mutane, tare da mutanen da ke sayen jariran.
Bayan da ka kama su ne suka shaida wa ‘yan sanda yadda suka yi cinikin yaran.
”Daya daga cikin wadda ta sayi jariran mai suna Favour Amaewhule ta ce ta sayi jaririn a kan kuɗi naira 700,000, inda aka bai wa mahaifin jaririn naira 350,000, sauran 350,000 ɗinn kuwa aka bayar da su ga tsohon kansilan tare da abokan hulɗarsa”, kamar yadda sanarwar ‘yan sandan ta bayyana.
A halin da ake ciki dai rundunar ‘yan sandan ta ce za ta ci gaba da gudanar da bincike domin gano ƙarin mutanen da ke wannan mummunar sana’a, domin daukar mataki a kan su.