Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta ce jami’anta sun kama wata mata mai shekaru 54 daga garin Jakana da ke karamar hukumar Konduga a jihar Borno bisa laifin safarar alburusai daga Buni Yadi zuwa Damaturu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Dungus Abdulkarim ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Litinin a Damaturu.
Ya ce a ranar 20 ga Oktoba, 2024, da misalin karfe 18:30, hedkwatar ‘yan sanda ta ‘A’, Damaturu, ta samu bayanan sirri game da wani da ake zargin dan bindiga ne da ke kan hanyar zuwa Damaturu.
Duba nan:
- Me yasa kashe Yahya Al-Sinwar yake da muhimmanci ga Isra’ila?
- Yan sandan Najeriya sun kama wasu ‘yan kasashen waje shida
- Police intercept gunrunner with 350 rounds of ammunition in Yobe
“Ayyukan da aka yi cikin gaggawa ya kai ga kutsa kai cikin motar Golf 3, kuma binciken kwakwaf ya gano harsasai 7.62 × 39 MM 350 da aka boye a cikin kayan wanda ake zargin.
Sanarwar ta kara da cewa, “A halin yanzu wanda ake zargin yana fuskantar tambayoyi na kwararru yayin da masu bincike ke kokarin bankado kungiyar masu aikata laifuka da kuma musabbabin fataucin,” in ji sanarwar.
A cikin sanarwar, kwamishinan ‘yan sandan, Garba Ahmed, ya tabbatar da kudurin rundunar na yaki da miyagun laifuka, don haka ya bukaci al’umma da su ci gaba da hada kai da jami’an tsaro.
“An shawarci jama’a da su kasance a faɗake kuma su kai rahoton abubuwan da ake zargi, mutane, ko abubuwa ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko kafa jami’an tsaro”, in ji shi.