Shugaban kwamitin aiwatar da shirin tallafin sufuri na karshen shekara na Shugaba Bola Tinubu, Dakta Dele Alake, ya bayyana cewa sama da fasinjoji 160,000 ne suka ci gajiyar shirin.
Alake, wanda kuma yake rike da mukamin ministan bunkasa ma’adanai, ya bay-yana hakan ne a cikin rahotonsa da aka gabatar a Jihar Legas.
Shirin wanda shugaba Tinubu ya kaddamar a ranar 19 ga watan Disamba ya shafi samar da zirga-zirga kyauta a hanyoyin jiragen kasan Nijeriya (NRC).
Bugu da kari, shugaban kasa ya rage kashi 50 na kudin sufuri ga fasinjojin da ke tafiya a kan hanyoyi 30 da masu gudanar da zirga-zirtar bas a karkashin kungiyar ‘Ludury Bus Owners of Nigeria’ (ALBON).
Da yake bayyana yadda shirin ya gudana, Alake ya jaddada gagarumar nasarar da aka samu.
Ya bayyana cewa ragin sufuri da Shugaba Tinubu ya aiwatar ya samu gagarumar nasara bisa la’akari da yadda ‘yan Nijeriya suka jin dadin lamarin.
“Tun daga ranar 21 ga Disamba zuwa 31 ga Disamba, 2023, alkaluma sun nuna cewa hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta dauki fasinjoji 71,000, yayin da motocin bas da ke aiki a karkashin ALBON sun dauki fasinjoji 77,122.
“Bas 652 da suka taso daga Oshodi na Legas sun dauki mutum 15,766. Wannan yana nufin cewa fasinjoji 163,878 ne suka amfana daga tallafin sufurin karshen shekara na shugaban kasa a cikin kwanaki 10.
“A yayin da fasinjoji a jirgin kasa suka samu gudanar da zirga-zirga kyautan, san-nan kuma fasinjoji take tafiya a kan hanya suka samu rangwame na kashi 50.”
Alake ya ce shirin na nuni ne da yadda shugaban kasar ke tausayawa da kuma kaunar ’yan Nijeriya wadanda suka kuduri aniyar gudanar da tafiye-tafiye a karshen shekara.
Ministan ya ce shirin yana kuma da nufin rage wa ‘yan kasar matsalar kudi, wadanda a cewarsa suna fuskantar wasu kalubale na tattalin arziki saboda bala’in da duniya ke fama da shi da kuma wasu abubuwan cikin gida.
Ya kara da cewa kwamitin ya dauki wasu matakai na gyara domin magance wasu kurakuran da aka gano wajen aiwatar da shirin, kamar kara wasu hanyoyi guda bi-yu da kuma jawo wasu masu ruwa da tsaki na motocin bas.
Source: LEADERSHIPHAUSA