‘Yan Najeriya na kokawa kan karancin sababbin takardun kudin da gwamnati ta kaddamar
Kwanaki 17 bayan da aka fitar da sabbin takardun kudin Najeriya, na Naira 200 da 500 da kuma 1, 000 da babban bankin kasar, ya yi, yawancin ‘yan kasar na cewa har yanzu ba su taba ganin sabon kudin ba ballantana ma su rike.
Da dama daga cikin ‘yan kasar sun nuna damuwarsu dagane da yadda sabon kudin ke wahala, ko a bankuna da wuraren cirar kudi na ATM.
Jama’a na nuna damuwar ne yayin da ya rage kasa da kwana 28 a daina amfani da tsoffin takardun kamar yadda babban bankin kasar ya sanar a kwanakin baya.
Wakilin BBC ya ziyarci wasu gundumomin da ke kwaryar birnin Abuja, inda ya tambayi wasu ‘yan kasar bin da suka fahimta daga karancin sababbin takardun kudin.
A Unguwar Area 2, wani mutum mai suna Alhaji Haruna ya ce, “Gaskiya na ganta a hannun wani mutum a Kano cikin makon da ya gabata, amma ni ban rike ta da hannu na ba, domin har banki na je cirar kudi amma ban ganta ba.”
Ya yi fatan takardun za su shiga hannunsa bayan sun wadatu a cikin kasa.
Wani mai suna Isma’il kuwa ya ce ya sami mallakar takardun kudi,
“Na same su a hannun wani mai sana’ar POS ne, na sami kimanin naira 20,000, sai dai takarar dubu daya ne kawai na samu.”
Sai dai ya ce bai gamsu da yawan takardun kudin ba kawo yanzu.
Wani mai sana’ar POS a Unguwar Area 10 ya ce ba ya samun wadannan kudaden.
“Suna na Mallam Abubakar. Ina sanar POS ne amma ko a banki ba a taba bani sababbin takardun kudin nan ba, domin idan naje, tsofaffin ake ba ni.”
Ya ce jama’a masu yawa na tambayarsa ko yana da sababbin takardun kudin.
Wakilin BBC ya kuma tafi titin Herbert Macaulay da ke Gundumar Wuse, inda ya ziyarci wata na’urar da ake cirar kudi ta ATM a gaban wani banki.
Ya tattauna da wasu mutane, kuma sun ce masa ko a bankin ma babu sababbin takardun kudin.
“Suna na Rachel Heg, kuma ban sami sababbin takardun kudin ba, domin ni kaina ban taba ganin sabon kudin ba, shi yasa na zo nan domin in ciro su ko na dace.”
Haka dai lamarin ya kasance ga wasu mazauna birnin na Abuja, kuma kamar wannan matar, yawancinsu sun bayyana rashin jin dadinsu kan al’amarin.
Ranar 9 ga watan Janairun nan ne gwamnatin Najeriya za ta fara aiwatar da wani umarnin babban bankin kasar na takaita yawan kudaden da ‘yan kasar za su iya karba daga asusu ajiyarsu na banki, matakin da ya janyo cece-ku-ce a fadin kasar.