‘Yan fashi sun kashe mutum 12 da sace dagaci a Bakori, an kuma kashe mutum 44 a Neja.
Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan fashin daji ne sun afka wa yankin Ƙaramar Hukumar Bakori da ke Jihar Katsina a arewacin Najeriya, inda suka kashe mutane da dama tare da sace dagacin garin Guga ranar Litinin da dare.
Wani mazaunin garin da muka sakaya sunansa saboda tsaro ya shaida wa BBC Hausa cewa maharan sun tafi da matarsa da ‘yarsa sannan suka ƙona gidansa.
Maharan sun afka wa garin na Guga da misalin ƙarfe 10:30 suna harbe-harbe.
“Duka shagunan garin sun ƙona su,” a cewar Mahadi. “Sun ƙona gidaje. Ni kaina nan sun ƙona min gida, an kama min mata, an kama min ‘ya ‘yar ƙarama, an kama min ƙanne.”
Kazalika, ‘yan fashin sun tafi da mai garin Guga Alhaji Umaru Bala. Daga cikin wasu manyan mutanen garin da aka sace a harin akwai Alhaji Usman Babanyara da Ado Hassan da Malam Umaru Ɗan-Asabe.
- Yadda ƴan sanda suka kama ‘babban mai kai wa Bello Turji makamai’
- ‘Yan bindiga sun tarwatsa mutanen garuruwa uku a Zamfara
- Abin da ba ku sani ba kan manyan dazukan da ƴan fashi ke ɓuya a Najeriya
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Katsina bai tabbatar ko musanta faruwar lamarin ba, yana mai cewa zai tuntuɓa idan ya bincika.
Malam Mahadi ya ƙara da cewa ya zuwa yanzu an yi jana’izar mutum 12.
Haka nan ya ce waɗanda aka sace sun kai kusan mutum 50 duk da cewa ba su gama tantancewa ba, kuma ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ‘yan bindigar ba su tuntuɓe su ba.
“Shekaran jiya ma (Lahadi) sun shiga wani gari sun kashe mutum 10 amma babu wanda ya zaci cewa za su sake dawowa,” a cewarsa.
An kashe kusan 44 a Neja
Wasu rahotanni dajaridar Vanguard ta tattara sun bayyana cewa wasu hare-hare da ‘yan fashin dajin suka kai a Jihar Neja sun yi sanadiyyar kashe mutum kusan 44, ciki har da wani mai lalurar ido.
Sakataren Gwamnatin Jihar Neja Ahmad Matane ya tabbatar wa BBC faruwar hare-haren amma ya ce suna jiran cikakken bayani daga jami’an tsaro.
Maharan sun afka wa ƙananan hukumomin Shiroro da Munya ne a ranar Litinin, inda mazauna yankin suka faɗa wa jaridar cewa waɗanda aka kashe mafi yawansu mata ne da ƙananan yara a ƙauyukan Galadinma Kolgo da Erena da Chukuba da Allawa. Mutum 27 aka kashe a harin.
Kazalika, ranar Asabar maharan sun afka wa ƙauyukan da ke Ƙaramar Hukumar Munya tare da kashe mutum 16 a ƙauyukan Guni da Dazza da Zagzaga, a cewar rahoton na Vanguard.
Wani shugaban matasa a yankin, Jibril Allawa, ya ce ‘yan fashin dajin sun fara tattaunawa mutanen, inda suke neman kuɗin fansa naira miliyan 60.
“Kusan dukkan ƙauyukan da aka kai hare-haren yanzu sun zama kufai, mutanen sun koma gudun hijira a makarantar firamare da ke Gwada,” in ji shi.