Yan Boko Haram Fiye Da 500 Daga Shirin Raba Su Da Tsattsauran Ra’ayi Domin Sake Shigar Da Su Cikin Al’umma.
Mahukunta a kasar ta Nigeria ne su ka sanar da yaye tsoffin ‘yan kungiyar ta bokoharam su 559 a cibiyar bayar da horo da take a jihar Gombe,inda aka gudanar da kwarya-kwaryar biki a karshen makon da ya shude.
Tsoffin mayakan sun bayyana azamarsu ta yin bayayya ga Nigeria da tsarinta da a baya su ka yaka.
Tun a 2015 ne dai gwamnatin tarayyar kasar ta Nigeria ta fito da wani shiri na bayar da horo ga mayakan domin raba su da ra’ayin wuce gona da iri, da zai basu damar komawa su rayu a cikin al’umma.
READ MORE : MDD Ta Yi Tir Da Zartar Da Hukuncin Kisa Da Saudiyya Ta Yi Wa Wasu Mutane 81.
Daga cikin shirye-shiryen da ake gudanarwa a cibiyoyin bayar da horon da akwai koyar da sana’o’i, karatun addini da kuma horar da kwakwalensu domin raba su da tunanin wuce gona da iri.
Adadin wadanda aka yaye din sun kai 1,629.
READ MORE : Sojojin Isra’ila Sun Kashe Falasdinawa Biyu.