Rahotanni sun nuna cewar, makwanni biyu da suka gabata ne ‘yan bingan suka dinga shiga kauyukan, tare da kashe akalla mutane Mazauna kauyukan dubu hamsin, da sace shanu.
Sakamakon wannan hare-haren dubban mata dake karamar hukumar Sabon Birni sun yi gudun hijira zuwa sakatariyar karamar hukumar, da makarantar firamari na Abdulhamid dake Sabon Birni.
Jaridar Daily Trust ta wallafa labarin dake cewa, da yawa daga cikin wadannan ‘yan Gudun hijiran sun koma Tudun Sunnah a jihar Maradi dake jamhuriyar Nijar, yayin da akwai wasu ‘yan gudun hijiran da yawa, da suka so tafiya kasar ta Nijar, amma baza su samu damar tafiya ba, sabo da wasu dalilai.
Akalla mutane sama da dubu 50 daga karamar hukumar Sabon Birni dake Jihar Sokoton Najeriya suka tsallake iya zuwa Jamhuriyar Nijar domin samun mafaka sakamakon tabarbarewar tsaro ganin yadda Yan bindiga ke kai musu hari suna kasha su ba tare da kaukautawa ba.
Dan majalisar Jihar Sokoto dake wakilatar yankin Aminu Almustapha Boza ya bayyana haka inda yake cewa wadannan mutane da suka fito daga garuruwa 17 yanzu haka sun samu mafaka a kauyukan Tudun Sunnah da Gidan Runji dake karamar hukumar Maradi.
Boza yace akalla mutane sama da 300 Yan bindiga suka kashe a karamar hukumar Sabon Birni kawai daga bara zuwa bana.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar Boza yayi zargin cewar yayi iya bakin kokarin sa domin ganin gwamnan jihar su Aminu Waziri Tambuwal domin gabatar masa da rahoto akan irin ukubar da mutanen yankin sa ke fuskanta amma abin yaci tura.
Dan majalisar yace gwamnan yaki yarda ya bashi damar ganin sa ba tare da bayyana masa dalilin haka ba, yayin da yankin da yake wakilta ya zama dandalin ayyukan ta’addanci a jihar.