Yan bindiga da suka sace wani mai sayar da burodi a unguwar Ifawara a Osun sun nemi a biya N500,000 don fansarsa.
Wani mazaunin garin Wale Babatude ya tabbatar da sace mai tallar burodin ya ce da farko N5m aka nema amma aka rage zuwa N500,000.
Mutanen unguwar sun fara karo-karo domin hado kudin da za a ceto shi yayin da rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin.
Wasu masu garkuwa da mutane a Osun sun bukaci a biya su N500,000 a matsayin kudin fansar wani mai sayar da burodi da suka sace a safiyar Litinin.
Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka sace mai sayar da burodin da aka fi sani da ‘get in’ a Ifawara yayin da ya ke raba burodi da motarsa.
Kamar yadda bincike ta nuna, an sace wanda abin ya faru da shi ne misalin karfe 4 na asubahi a express road da ke Iwaraja a jihar, rahoton Vanguard.
Masu garkuwar, daga bisani sun aike da sako ga mutanen unguwar suna neman a biya su Naira miliyan 5 kafin a sako shi. Sai dai, wani mazaunin Ifewara, Wale Babatude ya shaidawa Vanguard cewa an rage kudin fansar zuwa N500,000 kuma mutanen unguwa sun fara karo-karo domin ganin an sako wanda aka sacen.
Kalamansa: “Da gaske ne, an sace ‘get in’ jiya, an tsinci motarsa da hajarsa, wato burodi, a titi kuma daga baya mun samu sako na neman biyan fansa ta Naira miliyan 5.
“Sai dai, daga bisani an rage kudin zuwa Naira 500,000 kuma mun fara yin karo-karo don tara kudin da za a sako shi.”
Martanin Rundunar Yan sanda kan lamarin Rundunar yan sandan Jihar Osun ta bakin mai magana da yawunta, Yemisi Opalola, ta tabbatar da afkuwar lamarin.
Zamfara: Za A Fara Rataye Yan Bindiga Da Masu Garkuwa Da Mutane.
A gefe guda, Gwamna Bello Matawalle na Zamfara ya rattaba hannu kan wata sabuwar doka ta yaki da yan bindiga da laifuka masu alaka a jihar, rahoton Daily Nigerian.
A karkashin dokar, wacce ta fara aiki nan take, ta tanadi hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk dan bindiga da laifuka masa alaka da hakan a Zamfara.
Da ya ke jawabi jim kadan bayan rattaba hannu kan dokar, Matawalle ya ce dokar na cikin matakai ne na yaki da yan bindiga, masu garkuwa da satar shanu a Zamfara.
Source:legithausang