Da asubar ranar Juma’a ne, ‘yan bindiga suka sake sace wasu dalibai da ke karatu a jami’ar tarayya da ke a garin Gusau a jihar Zamfara.
‘Yan bindigar da dama, sun kai farmakin ne a kauyen Sabon-Gida da ke a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.
Abun Al’ajabi: Wasu Mutanen Gari Sun Sace Matan ‘Yan Bindiga Da Nufin Ramuwar Gayya A Zamfara
Wani mazaunin kauyen Sabon-Gida mai suna, Nazeer Sabon-Gida, ya sheda wa kafar gidan talabijin ta Channels cewa, ‘yan bindigar sun kai farkin ne da misalin karfe 3 na asubar ranar Juma’a, inda a lokacin harin suka rinka harba bindigu ba kakkautawa.
A cewarsa, sun kai harin ne dakuna uku na kwanan daliban jami’ar, inda suka yi awon gaba, da daukacin daliban da ke kwana a dakuna uku na daliban.
Ya ce, har zuwa yanzu ba a tabbatar da adadin daliban da ‘yan bindigar suka sace ba.
Sai dai wata majiyar ta sheda wa gidan talabijin na Channels cewa, ‘yan bindigar sun fafata da dakarun soji a lokacin harin, amma hakan bai dakatar da ‘yan bindigar daga sace daliban ba.
A cewar majiyar, ‘yan bindigar sun raba kansu gida biyu ne, inda kashi daya ya fafata da sojin, kashi dayan kuma ya yi awon gaba da daliban.
In ba a manta ba, a watannin baya wasu daliban wannan jami’ar suka gudanar da zanga-zanga akan yawan sace daliban jami’ar.
Kauyen na Sabon-Gida, yana daura da jami’ar ne wadda take da kilo mita 20 daga garin Gusau.
An yi kokarin jin ta bakin mahukuntan jami’ar, musamman don a ji ta bakin mai magana da yawun jami’ar, Umar Usman, kan lamarin amma hakan ya ci tura.
Kazalika, rundunar ‘Yansandan jihar ba ta firar da wata sabuwar sanarwa kan kai harin ba.
Source: LEADERSHIPHAUSA