‘Yan bindiga sun kashe sojojin Najeriya 11 a wani sansaninsu a Kaduna.
Kimanin sojoji 11 sun rasa rayukansu yayin wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai kan wani sansanin sojojin Najeriya a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
Daruruwan ‘yan bindigan sun isa sansanin ne a kusa da kauyen Polwire a jiya Litinin kuma sun dauki wani lokaci suna musayar wuta da sojojin da ke cikin barikin.
Wata majiya daga rundunar soji Najeriya na cewa ‘yan bindigan sun isa sansanin ne bisa babura dauke da manyan makamai, ciki har da bindiga mai harba gurnati.
Majiyar ta ce an shafe sa’a biyu ana gwabzawa kafin ‘yan bindigan suka iya kore sojojin daga cikin sansanin.
“Mun rasa sojoji 11 kuma an raunata 19 yayin harin. Maharan sun kuma kona wasu motoci masu sulke uku bayan da suka mamaye sansanin”, inji wani jami’in sojojin Najeriya.
Majiyar ta kuma ce maharan sun kwashe makamai masu dama daga sansanin.
READ MORE : Mata 23 Sun Nutse A Cikin Ruwan Maliya A Kasar Sudan.
An kai sojojin da aka raunata zuwa babban asibitin Birnin Gwari da asibitin sojojin sama, yayin da aka kai gawarwakin wadanda suka mutu zuwa asibitin 44 da ke birnin Kaduna.
Sai dai ba a sami jin ta bakin kakakin rundunar sojin Najeriya Onyema Nwachukwu ba kan halin da ake ciki a yankin na Birnin Gwari bayan wannan mummunan harin.