‘Yan bindiga sun kashe mutum fiye da 130 a Jihar Filato.
Bayanan da ke fitowa daga Jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya sun nuna cewa an kashe mutum 135 yayin wasu hare-hare da ‘yan bindiga suka kai a wasu ƙauyuka ranar Lahadi.
Maharan sun far wa a aƙalla ƙauyuka hudu da ke Ƙaramar Hukumar Kanam a kan babura, inda suka dinga harbe mutane tare da ƙona gidaje masu ɗumbin yawa da kuma sace shanu.
Hukumomi ba su yi cikakken bayuani game da hare-haren ba.
Sai dai wani basaraken gargajiya a yankin ya shaida wa BBC cewa tuni aka gano gawar mutum 54 a kauyen Kukawa da kuma gawar mutum 34 a kauyen Gyambau.
Ya kara da cewa an kashe mutum talatin da daya a wasu kauyuka biyu.
Kana an kashe ‘yan kasto-da-gora akalla 16 a kauyen Shuwaka.
Bayanai sun nuna cewa cikin wadanda aka kashe har da kananan yara da matasa.
Mutane da dama ne suka ɓace sakamakon harin yayin da lamarin ya raba daruruwan mutane daga muhallansu.
Mazauna yankin sun yi zargin cewa an kwasshe kusan kwana guda kafin jami’an tsarto su kai musu dauki.
Sun kara da cewa wadannan su ne hare-hare mafiya muni da aka taba kai wa a yankin.
Hukumomi sun ce an tura ƙarin jami’an tsaro a yankin.
Jihar Filato ta sha fama da rikicie-rikice da ke da nasaba da ƙabilanci da kuma addini, amma a baya-bayan nan ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa sun ta’azzara matsalar.